Iran da Kasashen Musulmi za Su Hadu a Qatar domin Daukar Mataki kan Isra'ila

Iran da Kasashen Musulmi za Su Hadu a Qatar domin Daukar Mataki kan Isra'ila

  • Qatar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin Larabawa da Musulmi bayan harin Isra’ila a Doha
  • Taron zai tattauna kudurin da ministocin harkokin wajen Larabawa da Musulmi za su gabatar kan harin da ya hallaka mutane
  • Rahoto ya nuna cewa shugabannin kasashen Iran, Iraq da Turkiyya na daga cikin manyan baki da ake sa ran halartar taron a Doha

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Qatar – Gwamnatin Qatar ta tabbatar da shirin karbar bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da Musulmi domin nuna adawa ga harin Isra’ila a Doha.

Wannan mataki ya zo ne bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu jagororin Hamas a babban birnin kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida.

Shugabannin Qatar yayin jana'izar wadanda suka rasu a harin Isra'ila
Shugabannin Qatar yayin jana'izar wadanda suka rasu a harin Isra'ila. Hoto: @PeninsulaQatar
Source: Twitter

Tashar labaran Qatar ta QNA ta wallafa cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Dr Majid bin Mohammed Al Ansari ne ya sanar da taron.

Kara karanta wannan

Shanu sun cika Abuja: Fadar shugaban kasa, Sultan sun gana da Miyetti Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Majid ya ce taron na da muhimmanci wajen nuna hadin kai da goyon bayan kasashen Musulmi ga Qatar a fuskantar abin da ya kira “tsagerancin Isra’ila”.

Kasashen Musulmi za su hadu a Qatar

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, da Firayim Ministan Iraki, Mohammed Shia al-Sudani, za su kasance a Doha domin wannan muhimmin taro.

Rahoton Times of Israel ya nuna cewa shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ma yana Doha, kodayake ba a tabbatar da halartar sa a taron ba tukuna.

Bisa ga sanarwar da aka fitar, an tsara wannan taro ne domin nuna adawa kai tsaye ga Isra’ila da kuma jan layin gargadi cewa irin wannan hari ba za a amince da shi ba.

Harin da Isra'ila ta kai kasar Qatar

Harin da Isra’ila ta kai a Doha ya yi sanadiyyar mutuwar mambobin Hamas guda biyar tare da wani jami’in tsaro na Qatar.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi barazanar sake kai hari Qatar, ya kafa wa kasar Larabawan sharadi

Wannan lamari ya jawo suka daga kasashen duniya da dama ciki har da na Gabas ta Tsakiya, wadanda galibinsu abokan hulda ne na Amurka, wadda ita ce babbar abokiyar Isra’ila.

Qatar dai na taka rawar gani a rikicin Gaza tare da Amurka da Masar a matsayin masu shiga tsakani.

Wajen da Isra'ila ta kai hari a kasar Qatar
Wajen da Isra'ila ta kai hari a kasar Qatar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin masana kan harin Isra'ila

Wani mai sharhi a London, Andreas Krieg ya bayyana cewa hare-haren Isra’ila sun kasance “kutse cikin hurumin kasashe” da kuma kai hari kan diflomasiyya da kanta.

Ya ce wannan taro na Doha na da nufin aika sako ga Isra’ila cewa ba za a amince da irin wannan al’amari a matsayin dabi’a ba.

Legit ta tattauna da Ibrahim Adamu

Wani mai bibiyar abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, Ibrahim Adamu ya ce kamata ya yi ƙasashen Larabawa su fara hada makamai kamar yadda Iran ta yi.

Ibrahim ya ce:

"Ba a cika matsawa kasashen da suke da makamai ba. Ya kamata su ma su fara hada makamai domin kare kansu da yankinsu.
"Tunda Iran ta hada makamai ta huta da zama cikin fargaba."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Kasashe sun nemi kafa kasar Falasdinu

A wani rahoton, kun ji cewa kasashen duniya 142 sun goyi bayan kafa kasar Falasdinawa a Gaza domin kawo karshen zubar da jini.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya, Faransa da Saudi Arabia na daga cikin kasashen da suka amince da kudirin.

A daya bangaren, kasar Amurka wacce ita ce babbar kawar Isra'ila ta ce ba ta amince da kafa kasar Falasdinawa ba a Gaza.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng