Duniya Ta Sauya: An Nada ‘AI’ a Matsayin Minista domin Dakile Cin Hanci a Albaniya
- Firayim Ministan Albania, Edi Rama, ya tabbatar da sabon salo a gwamnatinsa domin dakile cin hanci da ake fama da shi
- Rama ya naɗa na'urar 'AI' mai suna Diella a matsayin minista domin kula da kwangilolin gwamnati da hana cin hanci
- Diella ta fara aiki a matsayin mataimakiyar AI kan dandalin e-Albania, tana taimaka wa jama’a da takardu da rage bata lokaci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tiranë, Albania - Gwamnatin kasar Albania ta kawo sabon salo a gwamnati domin tabbatar da kula da ayyukanta cikin sauki.
Firayim Minista, Edi Rama ya naɗa sabon minista na musamman da zata kula da kwangilolin gwamnati, wanda ba zai karɓi rashawa ko samun barazana ba.

Source: Getty Images
Albaniya ta nada AI a matsayin minista
Rahoton Reuters ya ce an nada na'urar AI ne domin kula da gwangililon da kuma kokarin dakile cin hanci a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edi Rama ya bayyana cewa an ƙirƙiri Diella ta hanyar fasahar AI, wacce za ta kula da duk kwangilolin gwamnati tare da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce:
“Diella ita ce minista ta farko da ba za ta bayyana a taron majalisar zartarwa ba kamar saura ba, saboda an kirkireta ta ne ta fasahar AI.
"Wannan matakin samar da ita a matsayin minista zai tabbatar da gaskiya da hana cin hanci a harkokin gwamnati."

Source: Twitter
Zargin cin hanci da rashawa a gwamnatin Albaniya
An daɗe ana zargin Albaniya da yawaitar rashawa cikin kwangiloli, lamarin da ke kawo cikas ga burin shiga Tarayyar Turai kafin shekarar 2030.
Sai dai gwamnati ba ta fayyace yadda za a gudanar da kulawa a kan Diella ba, ko kuma yiwuwar a iya sarrafa wannan fasaha ta AI.
Tun farko Diella ta fara aiki a matsayin mai taimako ta AI a shafin e-Albania, inda take taimakawa jama’a da takardu cikin sauƙi, The Guardian ta ruwaito.
Martanin mutane kan nada AI minista
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon salo inda wasu ke yabon ci gaba da aka samu wasu ko ke sukar lamarin
Wasu sun nuna shakku, inda wani ya rubuta cewa nan ba da jimawa ba ita ma Diella za a birkita ta ta manta da maganar yaki da cin hanci.
Wani ya ce:
“Ita kanta Diella sai an lalata ta kuma an mayar da ita mai cin hanci idan dai a Albania ne.”
Za a kaddamar da sabuwar majalisa ranar Juma’a, amma ba a tabbatar da ko gwamnati za a kada kuri’a a kai a ranar farko ba.
Fasahar AI: Amurka ta ba Najeriya shawara
Kun ji cewa kasar Amurka ta shawarci Najeriya kan horas da dakarun sojinta wajen amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) yayin kai hare-hare.
Amurka ta kuma jajanta wa al'ummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, inda aka kai harin sojoji bisa kuskure.

Kara karanta wannan
Matasa sun bankawa majalisa wuta, an tilastawa Firayim Minista yin murabus a Nepal
Kasar ta ce yin amfani da fasahar AI zai kawo karshen kai wa fareren hula hari, kasancewar fasahar na iya bambance dan ta'adda da farar hula.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

