Lamari Ya Kazanta: Masu Zanga Zanga Sun Kona Matar Tsohon Firayim Minista a Nepal

Lamari Ya Kazanta: Masu Zanga Zanga Sun Kona Matar Tsohon Firayim Minista a Nepal

  • Masu zanga-zanga a Nepal suna ci gaba da barna bayan fira ministan kasar ya yi murabus saboda yadda aka taso shi a gaba
  • Matasa da ke zanga-zanga sun ƙona gidan tsohon Fira minista Jhalanath Khanal, inda matarsa Rabi Laxmi Chitrakar ta ke ciki
  • Rahotanni sun tabbatar da matar ta rasu sakamakon gobarar da ta tashi wanda aka kai ta asibiti kafin likita ta tabbatar da mutuwarta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kathmandu, Nepal - Rikici na ci gaba da kamari a Nepal da ke Nahiyar Asia bayan barkewar zanga-zanga a fadin kasar.

Lamarin ya munana bayan rasa ran matar tsohon Fira ministan kasar sanadin kona da aka yi a cikin gidanta wanda ya tayar da hankula sosai.

Yan zanga-zanga sun kona matar tsohon fira ministan Nepal
Tsohon fira ministan Nepal da ya yi murabus bayan zanga-zanga ta yi tsanani. Hoto: Sanjit Pariyar/NurPhoto.
Source: Getty Images

Zanga-zanga ta yi sanadin matar tsohon fira minista

Kara karanta wannan

An dura kan Bashir Ahmad game da sukar kiran zanga zanga a Najeriya kamar Nepal

An tabbatar cewa masu zanga-zangar sun rufe Rabi Laxmi Chitrakar a cikin gidan kafin daga bisani su kunna wuta, lamarin da ya yi muni matuƙa, cewar rahoton India Today.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabi Laxmi Chitrakar wacce ita ce matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta mutu a gidansu dake unguwar Dallu, Kathmandu.

An garzaya da ita Asibitin Kirtipur Burn, amma ta rasu sakamakon raunukan gobarar da ta samu a lokacin harin.

Menene musabbabin zanga-zanga a Nepal?

Hakan ya faru ne bayan gungun matasa da suka gaji da lamarin cin hanci suka fara zanga-zanga, suna neman a tsige jami’an gwamnati bisa laifin cin hanci da nuna son kai.

Tun daga Litinin, an ruwaito mutuwar mutum 22 yayin da sama da 300 suka samu rauni a rikicin da ya barke a ƙasar.

Kungiyar Amnesty International ta zargi ’yan sanda da amfani da harsasan gaske wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke neman sauyin gwamnati.

Bidiyon da aka yada ya nuna yadda aka jefa abubuwa masu fashewa a gidajen tsofaffin Firaminista, ciki har da K.P. Sharma Oli da Deuba.

Fira ministan Nepal ya yi murabus bayan zanga-zanga
Masu zanga-zanga a Nepal yayin arangama da jami'an tsaro. Hoto: Sunil Pradhan/Anadolu.
Source: Getty Images

Zanga-zanga: Halin da ake ciki a kasar Nepal

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fusata da zanga zangar adawa da 'ziyarar El Rufa'i' a Imo

Rahoton News24 ya ce wasu gine-ginen gwamnati sun rushe sanadin hari, ciki har da fadar shugaban ƙasa da kuma babban ofishin gudanarwar ƙasar.

Sakamakon wannan tashin hankalin wanda ya tilasta, Firaminista Oli, mai shekaru 73 yin murabus ya kara tabbatar da barazana da sauran jami'an gwamnati ke ciki.

Wasu ministoci ma sun bi sahunsa, ciki har da masu kula da harkokin noma, ruwa da harkokin cikin gida, domin rage matsin lamba a ƙasar.

A yanzu haka, hukumomi suna ƙoƙarin dawo da doka da oda, tare da kira ga jama’a su rungumi zaman lafiya da tattaunawa don kawo ƙarshen rikicin.

Firayim minista ya yi murabus a Nepal

Mun ba ku labarin cewa gungun matasa da suke yin zanga-zangar yaki da rashawa sun tilasta wa Firayim Minista a Nepal, K.P. Sharma Oli yin murabus.

Rikici ya tsananta a Nepal bayan kashe masu zanga zanga 19 da jikkata sama da 100 sakamakon harbe-harben ‘yan sanda.

Hotuna da bidiyo da aka gani sun nuna yadda aka cinna wa majalisar dokokin kasar wuta, sannan aka farmaki gidajen ministoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.