Wata Sabuwa: Amurka Ta Koro 'Yan Najeriya 2,330 daga Kasarta saboda Wasu Dalilai

Wata Sabuwa: Amurka Ta Koro 'Yan Najeriya 2,330 daga Kasarta saboda Wasu Dalilai

  • Hukumar ICE ta kori ‘yan Najeriya 2,330 daga Amurka a tsakanin shekarar 2014 zuwa farkon 2025, kamar yadda rahoto ya nuna
  • Kididdigar ICE ta nuna cewa an samu raguwar adadin 'yan Najeriya da aka kora daga Amurka daga 281 zuwa 138 a shekaru 11
  • Najeriya ce ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka yawan mutanen da aka kora daga Amurka a cikin shekarun nan da suka gabata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka – Hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta kori ‘yan Najeriya 2,330 daga kasar tsakanin shekarar 2014 zuwa farkon 2025.

Wannan na fitowa ne daga rahotannin shekara-shekara na hukumar da suka kunshi bayanai daga 2014 zuwa 2024, tare da ƙarin adadin da aka rubuta a farkon 2025.

Amurka ta koro 'yan Najeriya akalla 2,330 daga kasarta a cikin shekaru 11.
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da aka koro daga kasashen waje a filin jirgin sama, karkashin kulawar jami'an NEMA. Hoto: @nemanigeria
Source: Twitter

'Yan Najeriya da aka kora daga Amurka

Kara karanta wannan

Fetur: Yadda harajin Tinubu zai shafi ma'aikata, masu sana'a, 'yan kasuwa da sauransu

A 2014, hukumar ICE ta kori ‘yan Najeriya 261, amma zuwa 2024 adadin da ake kora ya sauka zuwa 138, raguwar da ta kai kashi 47.1 cikin 100, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotannin sun nuna cewa adadin wadanda aka kora ya kasance: 224 a 2015, 242 a 2016, kafin ya tashi zuwa 312 a 2017 da 369 a 2018, daga baya ya ragu zuwa 286 (2019) da 199 (2020).

Lokacin annobar COVID-19 ya kawo babban koma baya, inda aka kori mutum 78 kacal a 2021 da 49 a 2022. Sai dai a 2023 an samu ɗan karuwar adadin zuwa 152, sannan ya tsaya a 138 a 2024.

Adadin 'yan Najeriya ya fi yawa a Afrika

Kididdigar hukumar ICE ta tabbatar cewa Najeriya ce ta fi kowace kasa a Afirka yawan wadanda aka kora daga Amurka a tsawon shekaru 11.

Bayan Najeriya akwai Somalia (1,539), Ghana (1,380), Senegal (1,122), da Kenya (858).

Kasashen da ba a cika korar mutanen da ake kora daga Amurka sun haɗa da Burundi (41), Botswana (39), Eswatini (37), da Chad (36).

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su biya harajin N45 kan kowace litar fetur da suka saya daga 2026

Wasu kasashe irin su Madagascar (3) da Sao Tome & Principe (1) suna da mafi ƙanƙantar 'yan ƙasarsu daga aka kora daga Amurka.

An ce Najeriya ce a kan gaba a Afrika, a yawan mutanenta da aka koro daga kasar Amurka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: @officialABAT, @realDonaldTrump
Source: Twitter

Laruwar 'yan Najeriya da aka kora daga Amurka

Rahoton ya danganta karin korar da aka samu a wasu lokuta da shirin Electronic Nationality Verification (ENV), watau tantance 'yan kasar ta yanar gizo.

Wannan tsarin ya baiwa jami’an jakadanci damar tabbatar da bayanan mutum ta yanar gizo ba tare da zuwa ofishin IEC kai tsaye ba, abin da ya rage jinkiri wajen tantancewa.

Hukumar ICE ta kuma nuna cewa tana iya sake ƙara tsaurara matakai a nan gaba, lamarin da ka iya ƙara yawan korar.

Za a koro 'yan Najeriya 5, 144 daga Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana fargabar gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump za ta kori ’yan Najeriya 5,144 daga kasar.

Ana zargin cewa daga cikin wadanda abin ya shafa na da laifuffuka, wasu kuma sun karya dokokin shige da fice yayin zamansu a Amurka.

A kokarin yayyafa ruwa ga wutar, gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti domin shawo kan lamarin musamman idan aka koro 'yan kasar na ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com