Sabuwar Rigima: Trump na Son Kawo Matsala yayin da 'Yan Iran za Su Shiga Amurka
- Gwamnatin Trump ta hana Mahmoud Abbas da tawagarsa takardar biza domin halartar taron UN da ake shirin yi
- An ce Iran, Sudan, Zimbabwe da Brazil na iya fuskantar ƙarin takunkumi kan tafiya Amurka yayin babban taron
- Rahoto ya nuna cewa ana duba yiwuwar hana jakadun Iran shiga shagunan Costco da Sam’s Club sai da izinin Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugabancin Donald Trump na ƙara tsaurara matakan shige da fice kan wasu ƙasashe yayin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da taron UN ne a kasar Amurka a ranar 22 ga Satumba, 2025.

Source: Getty Images
Rahotan CNN ya tabbatar da cewa an riga an hana shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, da tawagarsa biza, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya.
Wani rahoton ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana yiwuwar saka takunkumi ga tawagar Iran, Sudan, Zimbabwe da ma Brazil, duk da matsayin da ƙasar ke da shi a tsarin UN.
Me Donald Trump zai yi wa 'yan Iran?
Rahoto ya nuna cewa gwamnatin Trump na shirin ƙuntata wa ’yan ƙasashen da ke da takardar izinin zuwa Amurka da kuma waɗanda ke neman shiga domin taron UN.
Wannan wani sabon salo ne na tsaurara tsarin bizar kasashen waje da gwamnatin shugaba Trump ke yi.
Jakadun Iran, waɗanda tuni ake ƙuntata musu a New York, na iya fuskantar ƙarin dokoki, ciki har da hana su shiga shagunan saye da sayar da kayayyaki masu yawa kamar Costco da Sam’s Club.
Dalilin takunkumin shaguna a Amurka
Shagunan Costco da Sam’s Club na da matuƙar amfani ga jakadun Iran domin suna sayen kayayyaki masu yawa waɗanda ba su samuwa a ƙasarsu cikin sauƙi.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Wani rahoto daga Arab News ya kara da cewa suna aika wasu daga cikin kayan zuwa gida saboda farashin shagunan ya fi araha.
Sabon shirin zai bukaci jakadun neman izinin ma’aikatar harkokin wajen Amurka kafin sayayya a irin waɗannan shagunan, matakin da zai ƙara kuntata musu rayuwa a lokacin zamansu.
Matsayar Trump kan shugaban Brazil
Har yanzu ba a tabbatar ba ko sababbin takunkumin za su shafi shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ko dai ’yan tawagarsa ne kaɗai ba.
Brazil dai ita ce ƙasa ta farko da ke gabatar da jawabi a kowane buɗe babban taron UN, yayin da Shugaban Amurka ke jawabi na biyu bisa al’ada.

Source: Facebook
Wani abu da ake gani a matsayin abin mamaki shi ne haɗa Brazil cikin jerin ƙasashen da za a iya saka wa wannan takunkumi, duba da matsayinta a diflomasiyyar duniya.
Shugaban Amurka na son korar mutanen Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana wani shiri da zai ba shi damar korar Falasdinawa a Gaza.

Kara karanta wannan
Biafra: An daure shugaban 'yan a ware da ya fara hargitsa Najeriya a kasar Finland
Trump ya ce zai ba Falasdinawa makudan kudi domin su kaura zuwa kasashen da za a kama musu haya.
Duk da cewa Trump ya nuna bukatar son hakan, ana hasashen cewa kasashen duniya da dama ba za su goyi bayansa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
