Rigima Ta Barke bayan Tono Gawar Malamin Musulunci a Kabari Aka Kona Ta
- Rundunar ‘yan sanda ta fara farautar masu tsattsauran ra’ayi bayan sun tono kabarin malami Nurul Haque
- Shaidun sun ce an tono gawar Nura Pagla inda aka ƙona ta, lamarin da ya haddasa arangama tsakanin magoya baya
- Gwamnatin rikon kwarya a kasar Bangladesh ta bayyana lamarin da abin takaici wanda ba za a lamunta ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dhaka, Bangladesh - Rundunar ‘yan sanda ta kasar Bangladesh ta fara farautar wasu mutane bayan daruruwan masu tsattsauran ra’ayi sun yi kaca-kaca da kabarin malami.
An tabbatar da cewa lamarin ya rincabe inda ya koma rikici mai tsanani da ya ajalin wani mutum guda.

Source: Facebook
Yadda aka tono gawar malamin Musulunci a Bangladesh
Tun bayan kifar da Sheikh Hasina a bara, an kai hare-hare a wuraren ibada, amma wannan karo an tono kabarin aka kona gawa, cewar Dhaka Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaida ya ce an tono gawar malamin Nurul Haque Molla aka ƙone ta, wannan lamarin ya jawo tada jijiyoyin wuya da kuma rasa rai.
Sufetan ‘yan sandan gundumar, Rajbari Md Kamrul Islam ya yi magana inda ya tabbatar da cewa:
“Mun fara gano masu laifi, kuma babu wanda za a bari ya ci bulus kan abin da suka aikata na bakin ciki,”
Menene dalilin tono gawar malamin a Bangladesh?
Rahotanni sun ce masu tsattsauran ra’ayi sun fusata ne saboda kabarin ya yi kama da Ka’aba.
Malamin ya yi ikirarin shi ne Imam Mahdi wanda mutane da dama ba su tare da abin da yake fada.
An birne shi ne a wurin ibadar sa da ke Rajbari bayan rasuwarsa a watan Agusta amma jana'izarsa ta fita daga al'adun musulmin Sunni.
Magoya bayansa sun ce za a gyara kabarin, amma kungiyar kwamitin Iman-Aqida Raksha ta kai farmaki bayan sallar Juma’a, ta tono gawar.
Sun ce:
“Kimanin mutane 2000 sun mamaye wurin da guduma da sanduna, suka lalata kabarin."

Source: Facebook
Gargadin gwamnatin kasa kan daraja rayuka
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani mutum ya mutu, mutane 50 sun jikkata sanadin rigimar da ta barke wanda ake ganin abin takaici ne.
An bayyana mutumin da ya mutu a matsayin Russell Molla, mai kula da kabarin, ba tare da alaƙa da malamin ba ko ta kusa ko ta nesa, RFI Hausa ta tabbatar.
Gwamnatin kasar Bangladesh ta ce lamarin “abin takaici ne”, tana mai nanata muhimmancin kiyaye darajar rayuwar mutane da ke kasar.
Abu Ahmed Faijul Kabir ya ce:
“Mun ga yunkurin hana shirye-shiryen al’adu, tozarci kan koyar da kiɗa, da lalata wuraren Sufi sun zama ruwan dare.”
Jirgin sojoji ya fado kan yara a Bangladesh
A baya, mun ba ku labarin cewa jirgin sojojin saman Bangladesh ya rikito kan makaranta yayin da ɗalibai ke tsakiyar karatu a Arewacin babban birnin kasar, Dhaka.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Rahotanni sun nuna cewa mutum 19 sun mutu, wasu sama da 160 sun samu raunuka sakamakon hatsarin da ya afku.
Gwamnatin ƙasar Bangladesh ta sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi tare da tallafawa duka waɗanda lamarin ya shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

