Daga Amurka Zuwa Najeriya: An Gano Kasashe 11 da Suka Fi Yawan Kiristoci a 2025
Kiristanci na ci gaba da zama addini mafi girma a duniya, inda ake kiyasin cewa mabiyansa sun kai biliyan 2.2 a 2025.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan na nufin cewa kusan mutum 1 cikin 4 a duniya Kirista ne, wadanda suka bazu a sassa daban daban na duniya.

Source: Getty Images
Kiristoci na kara karuwa a duniya
Ko da yake addinin ya samo asali ne a Gabas ta Tsakiya sama da shekaru 2,000 da suka gabata, yanzu yana da mabiya a nahiyoyin Amurka, Afirka, Turai da Asiya, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce yaduwar Kiristoci a sassan duniya ya faru ne sakamakon hijira, mulkin turawa, musayar al’adu da kuma sauyin addini.
Duk da kasancewar kasashen Yammacin duniya irin su Amurka na da tasiri, saurin karuwar jama’a a Afirka da sassan Asiya na kokarin sauya cibiyar tasirin Kiristanci zuwa Kudancin duniya.

Kara karanta wannan
Lahadi: Ruwan sama da iska mai ƙarfi zai sauka a Abuja, Neja, Yobe da wasu jihohi
Kasashe 11 da suka fi yawan Kiristoci
Bisa bayanan CIA World Factbook, Pew Research da UN World Population Prospects, ga jerin kasashen da suka fi yawan Kiristoci a 2025:
1. Amurka — Miliyan 219 (63%)
Amurka ta kasance kasa mafi yawan Kiristoci a duniya. Duk da raguwar kaso na mabiya, amma yawan jama’arta ya sa adadin ya ci gaba da karuwa.
2. Brazil — Miliyan 169 (79.5%)
Brazil na da Kiristoci mafi yawa a Latin Amurka, inda kusan 8 cikin 10 na al’ummar kasar ke bin addinin Kirista.
3. Mexico — Miliyan 118 (89.2%)
Kusan 9 cikin 10 na ’yan Mexico Kiristoci ne, abin da ya sa kasar ta kasance daya daga cikin kasashen da suke da tsauri kan Kiristanci.
4. Najeriya — Miliyan 109 (45.9%)
Najeriya ce kasa mafi yawan Kiristoci a Afirka, duk da cewa Musulmi sun fi Kiristcoi yawa a kasar da kada, ko a iya cewa suna kunnen doki.
5. Jamhuriyar Kongo — Miliyan 105 (93.1%)

Kara karanta wannan
Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil
Kusan dukkanin ’yan kasar Kongo Kiristoci ne, abin da ya sa ta kasance daya daga cikin kasashen da Kiristanci ya fi rinjaye a duniya.

Source: Getty Images
6. Philippines — Miliyan 100 (85.3%)
Kiristanci ya iso kasar lokacin mulkin mallakar Spain, kuma sama da 85% na ’yan kasar na bin addinin Kiristanci har yanzu.
7. Habasha — Miliyan 91 (67.3%)
Habasha na da tsohuwar al’adar Kiristanci tun zamanin farko, tare da Cocin Orthodox, inda akasarin jama’a ke bin addinin.
8. China — Miliyan 72 (5.1%)
Duk da cewa 5% kacal na ’yan kasar ke bin addinin Kiristanci, amma yawan jama’ar kasar ya sa ta shiga cikin kasashen da suka fi yawan mabiya.
9. Afirka ta Kudu — Miliyan 56 (86%)
Kiristanci ya mamaye kasar, inda aka hadu da bangarori daban-daban tare da al’adu na gargajiya.
10. Kenya — Miliyan 49 (85.5%)
Kiristanci ya yi tasiri sosai a Kenya, inda sama da 8 cikin 10 na al’ummar kasar Kiristoci ne.
11. Italiya — Miliyan 48 (80.8%)
Italiya, wacce ta zama gidan Paparoma da Cocin Katolika, har yanzu ta kasance kasa mai karfin Kiristanci, kodayake karuwar ra’ayin bauta ba tare da addini ba yana tasowa.

Kara karanta wannan
Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu
Tinubu ya saukaka wa Kiristoci zuwa Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamatin Bola Tinubu ta ce za a dawo ziyarar Kiristoci zuwa Isra’ila da Jordan daga watan Satumba, 2025.
Shugaban hukumar NCPC ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da rangwamen kashi 50 cikin 100, inda masu ziyara za su biya rabin kuɗin tafiya kacal.
NCPC ta tabbatar da cewa duk shirin kariya da tsaron lafiya ya riga ya kammala don tabbatar da zuwa da dawowar su lami lafiya.
Asali: Legit.ng