'Dan Shugaban Ƙasa Ya Sayar da Jirgin Gwamnati, Kotu Ta Ɗaure Shi Shekara 6 a Guinea
- Wata kotu a Equatorial Guinea ta samu Ruslan Obiang Nsue, ɗan shugaban ƙasa, da laifin sayar da jirgin sama mallakin gwamnati
- Yaron shugaban kasar zai shafe shekara shida a kurkuku idan bai biya diyya da tara ga gwamnati da kamfanin jirgin saman ba
- Wannan ba shi ne karo na farko da ’ya’yan shugaban ƙasar ke fuskantar shari’a kan cin hanci, almundahana da cin zarafin ofis ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Guinea - Wata kotun kasar Equatorial Guinea ta samu ɗan shugaban ƙasar, Ruslan Obiang Nsue, da laifin sayar da jirgin sama mallakin gwamnati.
Kotun ta gano cewa Ruslan Obiang Nsue ya sayar da jirgin, mallakin kamfanin jiragen sama na ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Source: Getty Images
An yanke wa yaron shugaban kasa hukunci
A ranar Talata, alkalin kotun ya yanke hukunci cewa Obiang Nsue, ɗan shekara 50 kuma tsohon darektan Ceiba Intercontinental, zai yi zaman gidan yari na shekara shida idan bai biya diyya ga gwamnati ba, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Baltasar: Kotu ta hukunta jami'in gwamnatin da bidiyoyin lalatarsa da mata suka yadu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Hilario Mitogo, daraktan watsa labaran kotun koli, Obiang Nsue zai iya kaucewa zaman gidan yari idan ya biya diyyar kusan dala 255,000 tare da tara da diyya ga kamfanin jirgin ƙasar.
Kotun ta samu dan shugaban kasar da laifin sayar da jirgin ATR 72-500 ga kamfanin Spain mai suna Binter Technic Company, inda ya karɓi kuɗin ya sa a asusun bankinsa na Spain.
Sai dai an wanke shi daga tuhume-tuhume na almundahana da cin zarafin ofis.
Bincike kan sayar da jirgin gwamnati
Bincike kan badakalar sayar da jirgin ya fara ne a watan Nuwambar 2022 bayan da hukumomin Guinea suka gano bacewar jirgin kasar.
An gano cewa an riga an cefanar da jirgin ga kamfanin lula da jiragen sama na Spain, a lokacin da gwamnatin Guinea ta kai jirgin gyara a 2018.
A yayin shari’ar, yaron shugaban kasar, Obiang Nsue ya amsa cewa:
"Na yarda cewa na rattaba hannu kan yarjejeniyar sayar da jirgin a kan kudi €250,000 amma na karɓi €125,000 ne kacal, wadanda na sanya su a asusun bankina na Spain."

Kara karanta wannan
Katsina: Yadda ƴan ta'adda su ka sace ɗiyar fitaccen ɗan kasuwar fetur da iyalinta

Source: Getty Images
Tuhume-tuhume kan 'ya'yan shugaban kasar
Masu gabatar da ƙara sun nemi a yanke wa Obiang Nsue hukuncin shekara 18 a kurkuku tare da tara ta CFA miliyan 500 ($847,000).
Wannan ba shi ne karo na farko da 'ya'yan shugaban ƙasar ke fuskantar hukunci ba, kamar yadda rahoton West Africa Weekly ya nuna.
A shekarar 2021, babban ɗan shugaban kasar, Teodorin Nguema Obiang Mangue, ya samu hukuncin shekaru uku a kotun Faransa bisa laifin almundahana, tare da tarar Euro miliyan 30.
Tinubu ya kulla yarjejeniya da Equatorial Guinea
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugaban Equatorial Guinea, Nguema Mbasogo sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya.
Shugaban kasar na Najeriya, a taron rattaba hannun, ya ce hadin gwiwar kasashen biyu za ta habaka samar da ayyukan yi ta bangaren iskar gas.
Haka kuma shugabannin biyu sun tattauna muhimman batutuwa da su ka shafi tsaro, samar da ayyukan yi da sauran hanyoyin samar da ci gaba ga jama'arsu.
Asali: Legit.ng