Trump Ya Kori Babban Sojan Amurka da Ya Tona Masa Asiri kan kai Hari a Iran
- Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya kori Janar Jeffrey Kruse bayan rahotonsa kan hare-haren Iran ya fusata Donald Trump
- Kruse ya ce hare-haren ba su lalata dukkan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran ba, abin da ya saba da ikirarin shugaba Trump
- Hakanan, an sallami wasu manyan hafsoshi biyu daga rundunar ruwa a wani yunkuri na Trump na tsaftace shugabancin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta sallami babban hafsan soja, Laftanar Janar Jeffrey Kruse, wanda ya jagoranci hukumar leken asirin tsaro ta ƙasa (DIA).
Rahotanni sun bayyana cewa an kore shi ne bayan rahotonsa kan hare-haren Iran ya sabawa ikirarin Shugaba Donald Trump.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ce an kori Kruse a ranar Juma’a tare da wasu manyan hafsoshin sojan ruwa biyu, a cewar jami’an tsaro da suka shaida wa manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korarren hafsun ya kasance shugaban DIA tun farkon shekarar 2024, kuma kafin haka ya riƙe manyan mukamai a fagen tsaro da leken asiri.
Yadda sojan Amurka ya fusata Donald Trump
Rahoton DIA ya nuna cewa hare-haren Amurka kan wuraren nukiliyar Iran a watan Yuni bai yi gagarumin barna ba, abin da ya saba da ikirarin Shugaba Trump cewa an rusa dukkan cibiyoyin.
Wannan rahoto ya jawo fushin shugaban ƙasa da wasu jami’an gwamnatinsa, lamarin da ya haifar da matsin lamba har zuwa korar Kruse daga mukaminsa.
Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da cewa Kruse 'ba zai sake ci gaba da zama shugaban DIA ba' ba tare da bayyana dalilin hukuncin ba.
Wasu sojoji da Trump ya kora a Amurka
Baya ga Kruse, Ministan tsaro, Pete Hegseth ya sallami wasu manyan sojoji da suka hada da Nancy Lacore da Milton Sands.
Rahoton Times of India ya nuna cewa dukkan hafsoshin sun bayyana cewa ba su samu cikakken bayani kan dalilin korarsu ba.
Wannan ya ƙara tunzura al’umma da majalisar dokokin Amurka, musamman ganin irin manyan mukaman da aka cire a lokaci guda.
Manyan 'yan siyasa sun nuna damuwa
Mataimakin shugaban kwamitin sirri na majalisar dattawa, Sanata Mark Warner ya ce korar manyan jami’an tsaro tana nuna yadda gwamnatin Trump ke siyasantar da lamarin tsaro.
Ya ce irin wannan tsari na iya zama barazana ga tsaron ƙasar, domin an juyar da aikin sirri daga abin kare ƙasa zuwa abin da ya danganci ra’ayin shugaba Trump.

Source: Twitter
Tun bayan fara wa’adinsa na biyu a watan Janairu, Trump ya sallami jami'ai da dama cikin rundunar sojojin Amurka.
A watan Fabrairu, ya sallami shugaban hafsoshin tsaro na ƙasa, Janar Charles Brown, ba tare da wani bayani ba.
Amurka ta koka kan albashin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yi magana kan lamuran tsaro da tattalin arziki da suka shafi Najeriya.
A wani rahoto da kasar ta fitar, ta ce sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba zai tabuka komai ba saboda karyewar darajar Naira.
Baya ga haka, Amurka ta zargi gwamnatin Najeriya ta gaza tabbatar da adalci a bangaren shari'a ga mutane a fadin kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

