Kwana Ya Kare: Alkali 'Mafi Tausayi a Duniya' Ya Rasu Yana da Shekaru 88

Kwana Ya Kare: Alkali 'Mafi Tausayi a Duniya' Ya Rasu Yana da Shekaru 88

  • Alkalin da ya yi fice a duniya saboda yadda yake tausaya wa jama'a a hukuncinsa, Frank Caprio ya riga mu gidan gaskiya
  • A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun bayyana cewa alkalin ya mutu yana da shekaru 88 a duniya bayan fama da jinya
  • Jama'a na yiwa marigayin lakabi da 'alkali mafi tausayi a duniya' saboda yadda yake da jin kai a hukuncin da yake yankewa mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Fitaccen alƙali a Amurka, Frank Caprio, wanda ya samu farin jini sosai a kafafen sada zumunta saboda tausayin da yake nuna wa mutane a kotu, ya riga mu gidan gaskiya..

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa har yanzu ba a hukunta 'masu' daukar nauyin ta'addanci ba': Minista

Alkalin wanda jama'a ke wa lakabi da 'alkali mafi tausayi a duniya' ya mutu yana da shekaru 88 da haihuwa.

Shahararren alkali a duniya, Frank Caprio.
Hoton fitaccen alkalin Amurka, Frank Caprio a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da iyalanaa auka wallafa a shafinsa na Instagram wanda ke da mabiya miliyan 3.2 a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, 2025.

Fitaccen alkali mai tausayi ya mutu a Amurka

Sanarwar ta tabbatar da cewa ya rasu yana da shekaru 88, bayan ya yi doguwar jinyar cutar daji.

A sanarwar an bayyana marigayi alkalin a matsayin mutumin da ake ƙauna saboda tawali'u da tausayin da yake nuna wa mutane.

Caprio, wanda aka fi sani da “alkalin da ya fi tausayin mutane a duniya,” ya shafe sama da shekaru 40 a matsayin alƙali a kotu da ke Providence, Rhode Island.

Yadda alkalin ya shahara a duniya

Ya shahara ne bayan bidiyoyinsa na yanke hukunci cikin murmushi da tausayi sun bazu a kafafen sada zumunta, inda aka kalle su sau sama da biliyan ɗaya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

Shekarun ƙarshe da ya yi a bakin aiki, kafin ya yi ritaya a 2023, ya yi su ne a cikin shirin talabijin mai suna Caught In Providence.

Kwana daya kafin ranar da ya rasu, Caprio ya wallafa sako daga gadon asibiti yana cewa:

"Abin takaici, na sake samun cikas. Na koma asibiti yanzu, kuma ina roƙon ku da ku sake tunawa da ni a cikin addu’o’inku.”

Caprio ya bambanta da sauran alkalan talabijin, wadanda galibi ake samu da tsauri da faɗa, domin shi ya kasance mai nuna tausayawa.

Yadda alkalin ke tausayawa jama'a a kotu

A wani shahararren bidiyo, ya soke tikitin tarar karya dokar hanya da aka bai wa wani mutumi da ya tsallaka danja bayan ya gano cewa yana samun ƙasa da $4 a awa.

A wani hukuncin kuma, ya saurari wata mata da ta rasa ɗanta cikin jimami, sannan ya soke duk tarar da aka kakaba mata wacce ta kai kusan $400, rahoton Sky News.

Marigayi mai shari'a Frank Caprio.
Hotun fitaccen alkalin Amurka mai tausayin al'umma a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayan rasuwarsa, Gwamnan jihar Rhode Island, Dan McKee, ya bayyana alhini da jimami, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane

"Marigayin ba kawai alƙali ba ne, alama ce ta jinƙai a kan kujerar shari’a, ya nuna mana abin da zai iya yiwuwa idan aka haɗa adalci da jinƙai.”

Jakadan Najeriya a Kamaru ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa karamin jakadan Najeriya a birnin Buea da ke jamhuriyar Kamaru, Ambasada Taofik Obasanjo Coker ya rasu.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da wannan rashi a wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa ya rasu ne ba zato ba tsammani a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, lamarin da ya girgiza al’ummar diflomasiyya ta Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262