"Mun Shirya Tsaf," Kasar Iran Tayi Maganar Tanadin Yakin da Tayi wa Israila

"Mun Shirya Tsaf," Kasar Iran Tayi Maganar Tanadin Yakin da Tayi wa Israila

  • Iran ta bayyana cewa ta kera sababbin makamai masu linzami da suka fi wadanda ta yi amfani da su a yakinta da Isra'ila
  • Ministan tsaron Iran ya bayyana cewa jamhuriyar musulunci a shirye take ta sake kai farmaki kan Iara'ila matukar ta sake tsokanarta da yaki
  • Ya ce Iran ba ta neman fada da kowa, amma za ta furkanci duk wanda ya kalubalance ta da iyakar karfinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin fuskantar duk wani sabon hari da Isra’ila ka iya sake kai mata nan gaba.

Iran ta sanar da cewa ta ƙera makamai masu linzami da suka fi ƙarfin waɗanda ta yi amfani da su a yakin kwanaki 12 da ya auku tsakaninta da Isra'ila a watannin baya.

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

Jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Hoton jagoran addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Kasar Iran ta shirya fuskantar Isra'ila

Ministan tsaron Iran, Aziz Nassirzadeh ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, 2025, kamar yadda jaridar gwamnatin Iran, IRNA ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mu muka kera makaman da aka yi amfani da su a yakin kwanaki 12 a wasu shekaru da suka wuce.
“Amma a yanzu mun ƙera kuma muna da makamai masu linzami da suka fi ƙarfin waɗanda muka yi amfani da su a baya, kuma idan makiyanmu auka sake tada yaƙi, ba shakka za mu yi amfani da su,” in ji shi.

Asalin rikicin kasar Iran da Isra'ila

A tsakiyar watan Yuni, Isra’ila ta fara kai hare-haren bama-bamai kan Iran, abin da ya tayar da yaki tsakanin ɓangarorin biyu.

Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da kuma jiragen yaƙi marasa matuki.

Hare-haren Isra’ila ya kashe manyan hafsoshin soji, masana nukiliya da daruruwan mutane, tare da lalata sansanonin soji da unguwanni a Iran.

Kara karanta wannan

N70,000: Amurka ta koka da karin albashi, matsalolin shari'a da tsaro a Najeriya

Amurka ta shiga yakin na ɗan lokaci ta hanyar kai hari kan wuraren nukiliyar kasar Iran, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Yaki na iya kara barkewa tsakanin Iran da Isra'ila

Sai dai daga bisani an tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila tun ranar 24 ga Yuni, amma jami’an Iran sun yi gargadi cewa sabon rikici na iya barkewa a kowane lokaci.

Sun jaddada cewa Tehran ba ta neman yaƙi da kowa, amma ta shirya tsaf idan aka ƙalubalance ta.

Jagoran addinin Iran da Firaministan Isra'ila.
Hoton jagoran addinin kasar Iran, da na firaministan Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Twitter

A ranar Litinin, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Farko, Mohammad Reza Aref, ya ce ya kamata Iran “ta kasance a shirye a kowane lokaci don fuskantar yaki.”

“Ba wai tsagaita wuta aka yi ta karewar yaki ba, kawai dai muna cikin wani yanayi na dakatar da hari,” in ji shi.

Rahotanni daga Iran sun nuna cewa sojojin ƙasar za su fara gwaji da atisaye na kwanaki biyu a ranar Alhamis, inda za a nuna makamai masu linzami masu gajeren zango da matsakaici.

Khamenei ya karawa 'yan Iran gwarin gwiwa

A baya, mun kawo rahoton cewa Ayatollah Ali Khamenei ya jagoranci wani biki mai cike da jimami domin tunawa da manyan hafsoshin sojan Iran da aka kashe a yaki da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Najeriya ta gaza hakuri, za ta buga da kasar Amurka kan sabuwar dokar biza

Jagoran addinin Iran, Khamenei ya gabatar da jawabi mai cike da karfin gwiwa da jajanta wa iyalan shahidan, yana mai cewa shahadar da suka yi ta kara wa kasar kima.

Ya jaddada cewa yayin yakin da ya dauki kwanaki 12 da Isra’ila ta kaddamar, al’ummar Iran sun nuna karfin guiwa da kishin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262