Kwana Ya Kare: Sanatan da ke Shirin Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu a Colombia
- Sama da watanni biyu da suka gabata, wani dan bindiga ya harbi Sanata Miguel Uribe Turbay a tsakiyar gangamin taron siyasa
- Wannan al'amari ya ja hankalin mutane a kasar Colombia musamman duba da cewa sanatan na da niyyar neman kujarar shugaban kasa
- Iyalan Uribe sun tabbatar da mutuwarsa yau Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025 a asbitin da aka kwantar da shi tun bayan harbin da aka masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Colombia - Sanata kuma mai neman takarar shugabancin ƙasa a Colombia, Miguel Uribe Turbay, ya rasu watanni biyu bayan an harbe shi a wani taron siyasa.
Iyalansa sun ce, Sanata Uribe, ɗan shekara 39 ya rasu a ranar Litinin a wani asibiti da ke Bogotá, inda yake karɓar magani tun bayan harin da aka kai masa.

Source: Facebook
Sanata Miguel Uribe ya mutu a Colombia
Matar Sanatan, María Claudia Tarazona ta tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mahaifin ‘ya’yana kuma abokin rayuwata, ka huta lafiya. Zan kula da ‘ya’yanmu. Ina roƙon Allah ya nuna min hanyar da zan iya rayuwa ba tare da kai ba.”
Tun a wurin taron siyasar aka kama wani matashi da ake zargi da hannu a lamarin a unguwar Bogotá, kuma daga baya hukumomin Colombia suka kara cafke mutane da dama.
Wane mataki aka dauka bayan harbin sanatan?
Rahotanni sun nuna cewa har kawo yanzu masu bincike ba su gano wanda ya ba da umarnin hallaka Sanata Miguel Uribe ba.
Bayan harin, an yi wa Uribe tiyata ta gaggawa, inda ya ci gaba da zama a dakin kulawa ta musamman har zuwa mutuwarsa.
Mahaifiyarsa, Diana Turbay, ta rasu lokacin da ‘yan sanda suka yi yunkurin ceto ta daga hannun ‘yan ta’adda masu safarar miyagun ƙwayoyi ƙarƙashin jagorancin Pablo Escobar da suka yi garkuwa da ita.
Masu garkuwar sun yi hakan ne don hana a mika su ga Amurka a lokacin, Uribe yana da shekaru biyar kacal.
“Idan mahaifiyata ta amince ta bayar da rayuwarta saboda wani dalili, ta yaya ni ba zan yi haka ba a rayuwata ta siyasa?” in ji Uribe a wata hira da aka yi da shi a bara.

Source: Facebook
Takaitaccen bayani kan Sanata Miguel Uribe Turbay
Sanata Uribe lauya ne mai digirin digirgir a fannin gudanar da harkokin jama’a daga Jami’ar Harvard, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Ya shiga harkokin siyasa yana da shekaru 26 da haihuwa a matsayin ɗan majalisar birnin Bogotá.
A shekarar 2022, ya samu mafi yawan ƙuri’u a jam’iyyar ra’ayin mazan jiya ta Democratic Center ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa Álvaro Uribe.
Tsohon shugaban kasar Romania ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasar Romania, Ion Iliescu, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025.
Marigayi Ion Iliescu ya shugabanci Romania tun a lokacin rikici, kafin daga bisani ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Gwamnatin ƙasar Romania ce ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan da al'ummar kasar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

