An Kashe Mai Yi wa Dakin Ka'aba Hidima da Makami Mai Kaifi a Birtaniya
- Matashi ɗan Saudiyya, Muhammad Al-Qassem, ya rasa ransa a Birtaniya a sanadiyyar caka masa wuka har lahira a birnin Cambridge
- Al-Qassem ya shahara da taimakawa mahajjata a Masallacin Harami, yana gudanar da ayyuka cikin tawali’u da sadaukar da kai
- Rahoto ya nuna cewa an cafke wasu mutum biyu dangane da kisan, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike sosai kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Britain - Masu hidima a Harami na cikin alhini da jimami bayan rasuwar matashi ɗan Saudiyya, Muhammad Al-Qassem, wanda ya shahara wajen taimaka wa mahajjata.
Al-Qassem ya rasa ransa ne a makon da ya gabata bayan an caka masa wuka sau da dama a cikin wani gini da ke birnin Cambridge, inda yake karatu a matsayin ɗalibi.

Asali: Facebook
Rahoton da Inside Haramain ya wallafa cewa matashin yana da shekara 20 da haihuwa a lokacin da lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hidimar da matashin yake yi a Ka'aba
Saudiyya ta bayyana cewa Muhammad Al-Qassem ya kasance mutum mai cikar kamala da halin kirki, wanda ke hidima ba tare da neman yabo ba.
A lokacin azumin Ramadan, Umrah da kuma lokacin Hajji, sau da dama za a gan shi yana taimaka wa dattawa da masu buƙata ta musamman a cikin Harami.
Wani daga cikin danginsa ya bayyana cewa:
“Ya kan kasance na farko da zai amsa kiran taimako. Ba ya ƙi wa kowa taimako, ko da kuwa ƙaramin abu ne. Bai taɓa daga murya ko faɗa ba, yana murmushi yayin da ya ke taimako.”
Hotunansa a kafafen sada zumunta sun sanya tunawa da irin tawali’unsa da jajircewarsa a cikin rigar masu aikin sa-kai a Harami, inda ya ke yin aikin ba tare da ɓata lokaci ba.
An kama mutum 2 a Birtaniya
Bayan aukuwar lamarin, an yi jimamin mutuwar Muhammad Al-Qassem daga sassa daban-daban na duniya.
Rundunar ‘yan sanda ta Birtaniya ta tabbatar da cafke mutum biyu bisa zarginsu da hannu cikin kisan.
Daya daga cikinsu ya fuskanci tuhumar kisan kai da kuma amfani da makami mai kaifi, kuma bincike na ci gaba domin gano hakikanin abin da ya faru.
Ofishin jakadancin Saudiyya ya tabbatar da cewa suna aiki tare da hukumomin Birtaniya, tare da shirya dawo da gawar marigayin gida domin yi masa jana’iza a Makkah.

Asali: Getty Images
Za a dawo da gawar Saudi daga Birtaniyya
Rahotanni sun nuna cewa ana shirin gudanar da jana’izarsa da zarar an dawo da gawarsa zuwa Saudiyya.
Tuni aka fara shirye-shiryen yi masa sallar jana’iza a Harami, inda ya kwashe shekaru yana hidima da tawali’u.
'Dan sarauta ya rasu a Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa masarautar Saudiyya ta sanar da rasuwar daya daga cikin 'ya'yanta da ya shafe shekaru yana rashin lafiya.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa marigayin ya shafe shekaru kimamin 20 yana sume ba tare da ya farfado ba.
Yayin da aka masa jana'iza a kasar Saudiyya, labarin shi ya karade kafafen sada zumunta musamman saboda doguwar jinyar da ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng