Romania: An Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Romania: An Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Romania ta shiga yanayin alhini da jimami bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Ion Iliescu yau Talata, 5 ga watan Agusta, 2025
  • Gwamnatin Romania ta tabbatar da wannan rashi a wata sanarwa, ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da shirin jana'izarsa
  • Marigayi Ion Iliescu ya shugabanci Romania tun a lokacin rikici, kafin daga bisani ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Romania - Tsohon shugaban ƙasar Romania, Ion Iliescu, ya riga mu gidan gaskiya yau Talata, 5 ga watan Agusta, 2025 yana da shekaru 95 a duniya.

Gwamnatin ƙasar Romania ce ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

Tsohon shugaban ƙasar Romania, Ion Iliescu.
Tsohon shugaban ƙasar Romania ya rasu yana da shekara 95 a duniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Marigayi Ion Iliescu, shi ne ya shugabanci kasar a lokacin rikice-rikicen sauyin mulki daga tsarin kwaminisanci zuwa dimokuraɗiyya, BBC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Mene aka yi mana?' Hadimin Ganduje ya ce za su tuhumi Tinubu a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ƙasar Romania ya rasu

A cikin sanarwar gwamnatin Romania ta ce:

“Cikin bakin ciki da juyayi gwamnatin Romania ke sanar da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Mista Ion Iliescu.”

Gwamnatin ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin da kuma duk masu kusanci da shi, tana mai cewa za a sanar bayanan jana’izarsa ta kasa a cikin kwanaki masu zuwa.

Yadda marigayin ya sha fama da jinya

An kwantar da Iliescu a asibiti tun farkon watan Yuni saboda cutar sankarar huhu (cancer).

A makon da ya gabata, asibitin da ke Bucharest inda ake duba lafiyarsa ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar yana cikin mawuyacin hali.

Karon ƙarshe da aka ga Iliescu a bainar jama’a shi ne a shekarar 2017, lokacin da masu gabatar da ƙarar da ake tuhumarsa suka gayyace shi domin amsa tambayoyi.

Taƙaitaccen tarihin shugaba Ion Iliescu

An haifi Iliescu a ranar 3 ga Maris, 1930, kuma ya kasance ministan matasa a lokacin mulkin tsohon shugaban kama-karya Nicolae Ceaușescu.

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Amma a shekarar 1970, ya fada komar gwamnatin Ceaușescu, wanda ta kai ga aka cire shi daga manyan mukamai.

Ya koma kan mulki a lokacin tashin hankalin juyin juya hali na watan Disambar 1989 wanda aka kifar da Ceaușescu, a cikin yanayi da har yanzu ba a fayyace ba.

A wannan lokacin ne Iliescu ya bayyana kansa a matsayin shugaban Kwamitin Ceton Ƙasa, watau gwamnatin rikon kwarya.

Daga bisani, Iliescu ya samu nasara a zaben dimokuraɗiyya na farko a watan Mayu 1990, kamar yadda Punch ta rahoto.

An sake zabensa a 1992 a wa’adi na biyu, sai dai ya sha kaye a 1996. Amma ya sake dawowa kan mulki a 2000 domin wa’adi na ƙarshe wanda kundin tsarin mulki ya amince da shi.

Fitaccen ɗan wasan kokawa ya mutu a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen ɗan wasan kokawa kuma masoyin Donald Trump, ya rasu yana da shekara 71 a duniya.

An ce Hogan, wanda sunansa na gaskiya shi ne Terry Gene Bollea, ya samu bugun zuciya ne a gidansa da ke Clearwater, Florida a Amurka.

Rahoto ya nuna cewa an dade ana yada jita-jita game da lafiyarsa, inda aka ce an kwantar da shi a asibiti kafin rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262