Haraji: Trump Ya Kawo Zazzafar Doka da Ta Shafi Najeriya kai Tsaye
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya haraji na kashi 15 a kan kayayyakin da ke shigowa daga Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa harajin ya shafi wasu ƙasashen Afirka kamar Ghana, Mozambique, Zimbabwe da Uganda
- Hakan na zuwa ne bayan shugaba Trump ya dakatar da harajin da ya kakaba wa kasashen duniya na kwana 90
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da sabon haraji na kashi 15 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya da wasu ƙasashe da dama.
Wannan matakin da Fadar White House ta sanar da shi a ranar Alhamis, yana cikin wani sabon tsarin haraji da Amurka ta samar.

Source: Getty Images
Fadar White House ta wallafa cewa sabon harajin zai shafi ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya, da sauran ƙasashe masu matakan haraji daga 10% zuwa 30%

Kara karanta wannan
Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harajin da Trump ya laftawa kasashe
Bayan Najeriya, sauran kasashen Afrika da harajin ya shafa sun haɗa da Ghana, Malawi, Zimbabwe, Zambia, Uganda, Mozambique, Mauritius, Lesotho da Madagascar.
Bisa wannan doka ta Shugaban Ƙasa Trump, za a fara aiwatar da harajin ne daga ƙarfe 12:01 na safiyar ranar 1 ga watan Agusta.
A cewar sanarwar, wasu ƙasashe kamar Afrika ta Kudu da Libya za su fuskanci haraji mafi tsauri har zuwa kashi 30 cikin 100, yayin da Tunisia ta fuskanci haraji na kashi 25 cikin 100.
Har ila yau, ƙasashe kamar Birtaniya za su fuskanci 10%, Indiya 25%, Japan 15%, da ƙasashen Asiya da dama ma an sanyawa musu harajin.
Kasashe da adadin harajin su
Baya ga Najeriya, wasu ƙasashen da aka laftawa harajin 15% sun hada da:
- Angola
- Botswana
- Côte d’Ivoire
- Democratic Republic of the Congo
- Japan
- South Korea
- Norway
- Uganda
- Zambia
- Zimbabwe da sauran su.
Haka kuma, akwai ƙasashe da aka sanya musu haraji mafi tsanani, ciki har da:
- Afrika ta Kudu: 30%
- Libya: 30%
- Tunisia: 25%
- India 25%

Source: Facebook
A cikin Afrilu, Trump ya fara gabatar da harajin 14% kan kayayyakin Najeriya, wanda daga bisani aka dakatar da shi tsawon kwanaki 90 domin ba da dama ga tattaunawar yarjejeniyar cinikayya.
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa wa’adin ya cika ne daidai da ranar Juma'a, 1 ga watan Agusta, 2025, lamarin da ya sa sabon tsarin ya fara aiki.
A halin yanzu dai za a jira sanarwa daga sauran kasashen da shugaba Trump ya laftawa haraji ko za su yi martani wajen laftawa kayan Amurka haraji ko a'a.
Iran ta tura sakon gargadi ga Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta fitar da sabon gargadi mai zafi ga kasashen Amurka da Isra'ila a kwanaki bayan kammala yakin da aka yi a baya.
Shugaban juyin juya hali na Iran ne ya yi martanin yayin taron kwana 40 domin tunawa da sojojin da Isra'ila ta kashe musu a yakin kwana 12 da suka yi.
Iran ta bayyana cewa Amurka da kawayenta suna adawa da ita ne saboda kara karfi da ta ke a bangaren fasaha da kimiya, ba wai domin nukiliya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
