Kisan Sojojin Iran: Ayatollah Khamenei Ya Fitar da Sabon Gargadi ga Isra'ila da Amurka
- Shugaban addini na Iran, Ayatollah Khamenei, ya jagoranci bikin tunawa da sojojin da Isra’ila ta kashe a yakin da suka yi
- Ya bayyana cewa shahidan yakin sun bar gagarumar gudumawa mai daraja ga kasar Iran da al’ummar Musulmi
- Khamenei ya soki Amurka da Isra’ila, yana mai cewa suna kin hadin kai da ci gaban kimiyya da addini a kasar Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya jagoranci wani biki mai cike da jimami domin tunawa da manyan hafsoshin sojan Iran da aka kashe a yaki da Isra’ila.
Bikin da aka gudanar a ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, 2025, ya zo daidai da cikar kwanaki 40 da rasuwar sojojin.

Source: Getty Images
Legit ta tattaro bayanan da shugaban ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafin shi na X a yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Khamenei ya gabatar da jawabi mai cike da karfin gwiwa da jajanta wa iyalan shahidan, yana mai cewa shahadar da suka yi ta kara wa Iran kima da karfi a idon duniya.
Ya jaddada cewa yayin yakin da ya dauki kwanaki 12 da Isra’ila ta kaddamar, al’ummar Iran sun nuna karfin guiwa da kishin kasa, wanda ya sa duniya ta gane girman da kasar ke da shi.
Ali Khamenei ya ce Iran ta nuna karfinta
Ayatollah Khamenei ya ce yakin da Isra’ila ta far wa Iran ya nuna yadda tsarin Jamhuriyar Musulunci ke da tsayayyen tushe da karko.
Rahoton Jerusalem Post ya nuna cewa shugaban ya kara da cewa duniya ta shaida cewa Iran ba kasa ce da za a iya dagula mata lissafi ba.
Ya tunatar da irin kalubalen da Iran ta sha tun bayan juyin juya hali na 1979, ciki har da yakin shekaru takwas, yunkurin juyin mulki, da wasu makirce-makirce na siyasa da tsaro.
A cewarsa, wannan karko da nasara da Iran ke samu ba wai da makami kawai ba ne, illa saboda amincewa da addini da kuma ilimi da suka zama ginshikan tsarin kasar.

Source: UGC
Maganar Khamenei kan Amurka da Isra'ila
Ayatollah Khamenei ya ce dalilin da ya sa makiya, musamman Amurka da Isra’ila, ke gaba da Iran shi ne kasancewar kasar tana kan turbar addini da ilimi.
A wata nasara da suka samu, ya ce Iran ta haɓaka yawan ɗaliban jami’a da ninki 10 tun bayan nasarar juyin juya hali.
Ya bayyana cewa ci gaban Iran a fannonin kimiyya da fasaha, da kuma tsayuwar daka wajen addini, shi ne abin da ke jawo kiyayya daga kasashen Yamma.
Ya ce sukan fake da batun haƙƙin ɗan Adam da nukiliya, alhali ainihin abin da suke adawa da shi shi ne hadin kan Musulmi da ci gaban kimiyya.
Trump ya gargadi Iran kan nukiliya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sake martani ga Iran kan mallakar nukiliya.
Shugaba Trump ya ce ba makawa za su sake kai hari Iran kamar yadda suka yi a baya idan ta cigaba da hada makaman kare dangi.
Ya kuma jaddada cewa sun yi nasarar ruguza cibiyoyin nukiliyar Iran duk da yadda wasu kafafen yada labarai ke karyata labarin.
Asali: Legit.ng

