Yaki zai Dawo Sabo: Trump Ya Yi Maganar Sake kai Hari Iran

Yaki zai Dawo Sabo: Trump Ya Yi Maganar Sake kai Hari Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta sake kai hari kan Iran idan akwai buƙatar hakan, bayan harin da ta kai makonni da suka wuce
  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa hare-haren Amurka sun lalata cibiyoyin nukiliya sosai, suna ci gaba da bincike
  • Yayin da ake daf da ci gaba da tattaunawa kan mallakar nukiliya a kasashen Turai, Iran ta ce ba za ta dakatar da haƙar sinadarin uranium ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kare harin da sojojinsa suka kai kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran a watan da ya gabata.

Shugaban kasar ya yi magana yana mai jaddada cewa Amurka za ta sake kai hari Iran idan bukatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan

'Juyin juya hali,' An kawo hanyar warware matsalolin Najeriya gaba daya

Trump ya ce zai iya sake kai hari Iran
Trump ya ce zai iya sake kai hari Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton ABC news ya nuna cewa Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya mayar da martani ga kalaman Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce cibiyoyin nukiliar kasar sun lalace sosai a sanadiyyar harin Amurka.

A cewar shugaba Trump:

“Za mu sake kai hari idan ya zama dole!”

Trump ya kare hare-haren Amurka a Iran

Shugaba Donald Trump ya nuna cewa sojojin Amurka sun yi aiki tukuru wajen tarwatsa cibiyoyin nukiliyar Iran.

Ya ce:

“Wannan ba wata barazana ba ce; mun lalata wuraren kamar yadda na faɗa tun da farko.”

Ya zargi gidan talabijin na CNN da rage girman nasarar da sojojin Amurka suka samu, yana mai cewa:

“Sojojinmu sun yi rugu-rugu da wancan ginin gaba ɗaya. Ya kamata CNN ta kori ɗaya daga cikin ‘yan jaridarta.”
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Sai dai CNN ta bayyana cewa, harin da Amurka ta kai bai yi wani dogon tasiri ba sai dai yana iya jinkirta shirin nukiliyar Iran da watanni kaɗan.

Kara karanta wannan

Harin da Amurka ta kai Iran bai lalata cibiyoyin nukiliya ba? Trump ya yi martani

Barnar da Amurka ta yi wa Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana a wata hira cewa an lalata wuraren nukiliya da yawa, kuma hukumar makamashin Iran na nazari kan irin barnar da aka yi.

Ya ce:

“An mana barna sosai. A halin yanzu muna nazarin irin barnar da aka yi.”

Ya kuma bayyana cewa Iran ba za ta daina haƙar uranium ba, yana mai cewa:

“Wannan abin alfahari ne a gare mu. Ba za mu daina ba saboda yana nuna kwarewar masana kimiyyar mu.”

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin sake sabunta tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Birtaniya, Faransa da Jamus a Istanbul ranar Juma’a mai zuwa.

Ambaliyar Amurka ta girgiza Trump

A wani rahoton, kun ji cewa an yi mummunar ambaliyar ruwa da ta halaka mutane da lalata dukiya mai yawa a Amurka.

Shugaban Amurka, Donlad J. Trump ya ziyarci wajen da aka yi ambaliyar tare da bayyana cewa abin ya yi muni sosai.

Kasashen duniya da suka hada da Najeriya sun yi wa Amurka jaje kan asarar rayuka da dukiya da ta yi a sanadiyyar ambaliyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng