Harin da Amurka Ta Kai Iran bai Lalata Cibiyoyin Nukiliya ba? Trump Ya Yi Martani

Harin da Amurka Ta Kai Iran bai Lalata Cibiyoyin Nukiliya ba? Trump Ya Yi Martani

  • Shugaba Donald Trump ya nace cewa harin bam da Amurka ta kai a birnin Tehran ya rushe gaba ɗaya cibiyoyin nukiliyar Iran
  • Yayin da Trump ya yi wannan ikirari, wasu rahotannin kafafen yada labarai sun ce wuri daya ne kawai harin ya yiwa illa ba duka ba
  • An ce Pentagon ta so Amurka ta kai hare-haren mako guda a Iran amma Trump ya ki amincewa da shawarar saboda wasu dalilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaba Donald Trump ya nace cewa harin bam da Amurka ta kai Tehran ya lalata gaba daya wuraren hada nukiliyar Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu rahotanni suka bayyana cewa wasu daga cikin cibiyoyin hada nukiliyar Iran sun tsira daga harin.

Donald Trump ya dage cewa harin da Amurka ta kai ya lalata cibiyoyin nukiliyar Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga al'ummar kasarsa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

"Mun lalata cibiyoyin nukiliyar Iran" - Trump

Kara karanta wannan

Sauya tsarin mulki: Ana son shugaban kasa ya dawo yin shekara 6 ba tazarce

Kafar labaran Reuters ta rahoto, Trump ya sake nanata ikirarinsa na cewa “an tarwatsa tare da lalata dukkanin wuraren nukiliya uku da ke Iran."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zai ɗauki shekaru kafin a iya dawo da su aiki, kuma idan Iran na son maido da su, zai fi musu kyau su fara sababbi a wasu wurare daban.”

- Donald Trump.

Harin bam da makamai masu linzami da Amurka ta kai ranar 22 ga Yuni ya auka kan cibiyoyin nukiliyar Iran da suka jawo ce-ce-ku-ce.

An ce harin na Amurka ya shafi babbar cibiyar haƙar uranium da ke Fordo, a kudu da birnin Tehran, da kuma wuraren nukiliya a Isfahan da Natanz.

Gwamnatin Amurka ta bayyana wannan harin, wanda aka kai tare da wani yunkuri daga Isra’ila kan gine-ginen soji da na nukiliyar Iran, matsayin rubdugun kawo karshen shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.

Ana da shakku kan tasirin harin Amurka

Iran dai ta nace cewa ba ta taɓa ƙoƙarin amfani da shirin makamashin nukiliya na farar hula domin kera makamai ba.

Ko da yake Trump na da’awar ya samu babbar nasara, wasu kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito rahotannin sirri da suka bayyana cewa ba lallai ne hakan ta tabbata ba.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba: Dattijon Arewa ya tsage gaskiya kan 'kurakuran' Buhari

Rahoton farko na binciken sirri da aka fallasa wa kafafen watsa labarai bayan harin da aka kai a baya, ya ce harin bai lalata muhimman sassan shirin nukiliyar Iran ba, sai dai ya jinkirta aikin na su da watanni kaɗan ne kawai.

Amma a farkon watan Yuli, ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta bayyana cewa hare-haren sun rage ƙarfin shirin Iran da shekaru daya zuwa biyu.

An ce Donald Trump ya ki amincewa da shawarar Pentagon na kai harin mako guda a Iran
Shugaban kasa Donald Trump ya nace cewa harin Amurka ya lalata cibiyoyin nukiliyar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi watsi da shawarar Pentagon

Rahoton da kafar NBC News ta fitar a ranar Juma’a shi ne mafi sabo da ke kawo shakku, inda ta ambaci binciken barnar da ya nuna cewa wurin aiki guda ɗaya ne kacal aka lalata sosai.

Rahoton ya ce sauran wurare biyu za a iya gyara su cikin watanni kaɗan kuma za su iya komawa haƙar uranium, kamar yadda wasu jami’an gwamnati biyar suka tabbatar.

Ta kuma ruwaito cewa tun da fari Pentagon ta tanadi wani shiri da zai kai hare-hare na makonni a Iran, sabanin na dare daya da Trump ya zartar a baya.

Rahoton ya ce, Trump ya yi watsi da shawarar Pentagon na kai hare-haren saboda fargabar asarar rayuka da kuma jefa ƙasar cikin rikici da Iran na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

NELFund: Gwamnatin Tinubu za ta bude dandalin taimakawa dalibai samun aiki

Kasa 1 da za ta kare Iran daga harin Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran ta dade tana tallafa wa kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a Gabas ta Tsakiya domin samun kariya daga tasirin Isra’ila da Amurka.

Bayan Isra’ila ta kai hari cikin kasar Iran, kawayenta kamar Hezbollah da Houthi sun yi shiru, ba su ma ce uffan ba a matsayin martani kan hare-haren.

Sai Rasha ce kaɗai ta fito ta nuna goyon bayanta ga Iran, inda ta yi gargaɗin cewa shisshigin Amurka zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici mai muni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com