Tashin Hankali: Mamakon Ruwan Sama Ya Jawo Ambaliya a Gari, Mutane 54 Sun Mutu

Tashin Hankali: Mamakon Ruwan Sama Ya Jawo Ambaliya a Gari, Mutane 54 Sun Mutu

  • Mutane 54 sun mutu cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Pakistan, yayin da adadin wadanda suka mutu a daminar bana ya kai 180
  • Gwamnatin kasar ta sanar da cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da yake sauka tun a ranar Laraba ne ya jawo ambaliyar
  • Hukuma ta shawarci jama’a da su tanadi abinci da magunguna, yayin da gwamnati ta ayyana hutu don kare rayukan 'yan kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Pakistan - Hukumar kula da bala'o'i ta Pakistan ta sanar da cewa ruwan sama mai yawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 54 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

A cewar sanarwar hukumar a ranar Alhamis, adadin waɗanda suka mutu a Pakistan ya kai kimanin 180 tun bayan shigowar damina a ƙarshen watan Yuni.

Ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama ta yi ajalin mutum 54 a Pakistan
Yadda ambaliya ta mamaye wani kauye a Kudancin Punjab da ke Pakistan. Hoto: Visual News Pakistan
Source: Getty Images

Ambaliya: Ana aikin ceto mutane a Pakistan

Kara karanta wannan

Kashim Shettima na shirin dauko gawar Buhari, jirgin sama ya yi hatsari a London

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya zuba ba kakkautawa a sassan lardin Punjab tun daga safiyar Laraba, wanda ya haddasa ambaliya da rushewar gidaje, inji rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin agaji sun yi amfani da jiragen ruwa don fitar da iyalai daga kauyuka da ke bakin koguna a ƙasar da safiyar ranar, amma ruwan ya fara ja da baya da yamma.

Tariq Mehbood Bhatti, wani manomi mai shekaru 51 a ƙauyen Ladian, ya ce:

“Yara suna ihu suna neman taimako, mata kuma sun tsaya a kan rufin gidaje, suna ɗaga mayafansu suna roƙon a cece su”.

An umurci mazauna yankunan da ke kusa da kogin Nullah Lai da ya ratsa birnin Rawalpindi, mai maƙwabta da babban birnin Islamabad, da su kaura bayan karuwar ruwan.

An shawarci jama’a da su tanadi abinci

Wata mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta ce:

“Tawagar ceto tana cikin shiri don komawa wuraren tare da kwaso ƙarin mutane”.

Hukumar kula da bala'o'i ta kasa (NDMA) ta bayyana cewa:

“Mazauna yankunan da ke cikin haɗari su tanadi kayan buƙata kamar abinci, ruwa da magunguna da za su ishe su na tsawon kwana uku zuwa biyar.”

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sha ruwa da tsawa a Kano, Yobe da jihohin Arewa 13 a ranar Lahadi

Gwamnatin Rawalpindi ta ayyana hutu a ranar Alhamis domin hana mutane fita daga gidajensu, yayinda hukumar hasashen yanayi ta yi gargaɗin cewa ruwan sama mai karfi zai ci gaba da sauka har zuwa Juma’a.

Hukumar hasashen yanayi ta gargadi mazauna Pakistan cewa ruwan sama zai ci gaba da sauka har zuwa Juma'a
Masu ababen hawa na kokarin yin zirga-zirga yayin da ambaliyar ta shiga garuruwan Pakistan. Hoto: JAN ALI LAGHARI / Contributor
Source: Getty Images

Mutuwar mutane da rushewar gidaje

Kimanin mutane 180 ne suka mutu, ciki har da yara 70, kuma kimanin 500 suka ji rauni tun farkon damina a ranar 26 ga Yuni, a cewar hukumar kula da iftila'o'i ta kasar.

Kakakin NDMA ta shaida wa AFP News cewa:

“A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 54 suka mutu, 227 kuma suka ji rauni a faɗin Pakistan. An fi samun mace-macen a Punjab."

Yawancin mace-macen sun faru ne sanadin rushewar gidaje sakamakon ambaliyar ruwan, yayin da kuma wasu da yawa suka mutu sanadiyyar wutar lantarki.

India ta harba makamai zuwa Pakistan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Indiya ta harba makamai masu linzami kan kasar Pakistan da Kashmir a ranar Laraba, 7 ga Mayu 2025.

Indiya ta ce ta kai harin ne kan wurare tara da ake kyautata zaton mafakar 'yan ta'adda ce a Pakistan, wadanda ta zarga da kai hari a Kashmir.

Sai dai Pakistan ta yi martani da cewa harin da Indiya ta kai ya yi ajalin fararen hula 26, yayin da ta samu nasarar harbo wasu jiragen yakin Indiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com