Rasuwar Buhari: Amurka Ta Rufe Ofishinta a Abuja, Saudiyya Ta Aiko da Sako Najeriya
- An rufe ofishin jakadancin Amurka a Abuja da Legas don karrama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu ranar Lahadi
- Amurka ta ce za ta sanar da sabon lokacin da za ta tuntubi wadanda suka cike bukatar biza kuma aka ce za a saurare su ranar 15 ga Yuli 2025
- A hannu daya, Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya aike da sakon ta'aziyya ga Shugaba Bola Tinubu kan rasuwar Buhari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Amurka ta rufe babban ofishin jakadancin ta da ke Abuja da kuma karamin ofishin jakadancin ta da ke birnin Legas a ranar Talata.
An rahoto cewa Amurka ta yi hakan domin girmama hutun da gwamnatin Najeriya ta bayar don girmama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu.

Source: Twitter
Amurka ta rufe ofisoshinta a Abuja, Legas
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Litinin, 14 ga Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Amurka, rufe ofisoshin jakadancinta zai nuna girmamawarta ga Najeriya da kuma karrama marigayi shugaban Najeriya, Buhari.
Sanarwar da Legit Hausa ta gani ta ce:
"Da wannan matakin ne muke sanar da cewa za a sake tsara lokaci don nazarin duk wani alƙawarin bayar da biza da aka shirya yi ranar 15 ga Yuli, 2025."
Amurka ta aika sako ga masu neman biza
Duk da hakan, Amurka ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa masu neman bizar za su samu sababbin kwanakin da za a tantance su nan ba da jimawa ba.
Ana sa ran Amurka za ta bude ofisoshin jakadancinta domin ci gaba da ayyuka bayan lokacin hutun da aka bayar a kasar.
Mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta ayyana Talata a matsayin ranar hutu don girmama Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti a Landan yana da shekaru 82.
Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya a matsayin zababben shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023, ya taba rike shugabancin kasar a lokacin soja tsakanin 1983 zuwa 1985.
Sarkin Saudiya ya aiko sako Najeriya
A wani jikon kuma, mai kula da masallatai masu tsarki biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya aike da sakon ta'aziyya da jajantawa ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Sarki Salman bin Abdulaziz ya ce ya kadu sosai da ya samu labarin rasuwar Buhari, inda ya jajantawa shugaban ƙasa, al'ummar Najeriya, da kuma iyalan mamacin, inji rahoton NTA News.

Source: Twitter
Manyan 'yan Najeriya da suka rasu a 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, daga Yuni zuwa Yulin 2025, Najeriya ta rasa wasu manyan mutane da suka taka rawar gani a fannonin shugabanci, ilimi da sarauta.
Cikin shahararrun da suka rigamu gidan gaskiya har da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da fitaccen ɗan kasuwa kuma attajiri, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Sauran sun haɗa da sarakunan gargajiya da masana a fannoni daban-daban, waɗanda mutuwarsu ta bar babban gibi tare da haddasa jimami a fadin ƙasa da ma ƙetare.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Cikin hawaye, Fatima Buhari ta isa Daura inda za a binne gawar mahaifinta
An fara tona kabarin Buhari a Daura
A wani labarin, mun ruwaito cewa, DSS, sojoji, ‘yan sanda da NSCDC sun mamaye sassa daban-daban na Katsina yayin da ake shirin karɓar gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an fara aikin tono kabari a wani yanki na gidansa da ke Daura, inda ake sa ran za a birne shi.
Haka zalika, an samar da shingen musamman a wajen da ake tono kabarin domin kare wurin da kuma sauƙaƙa kula da shi nan gaba.
Asali: Legit.ng

