Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da salloli 5 a masallatai, banda guda 2

Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da salloli 5 a masallatai, banda guda 2

Labari da dumi dumi ya ishe mu cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatar da sallolin farilla guda biyar a masallatai ta hanyar bayar da umarnin garkame dukkanin masallatan har baba ta ji

Shafin Haramain Sharifain na dandanin sadarwa na Facebook dake bayar da jawabi game da Masallatai guda biyu masu tsarki na Musulunci ne ya tabbatar da haka, inda tace majalisar manyan malaman kasar ce ta bayar da wannan fatawa.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da salloli 5 a masallatai, banda guda 2

Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da salloli 5 a masallatai, banda guda 2
Source: UGC

Majalisar Malaman ta umarci a garkame dukkanin Masallatai, tare da daina dukkanin sallolin farilla a masallatan, hatta sallar Juma’a, illa don kiran Sallah kawai, don haka ta umarci ladanai su dinga cewa “Sallu fi rihalikum” watau ku yi sallah a gida.

Sai dai gwamnatin ta amince da barin manyan masallatan Makkah da Madina guda biyu. Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne sakamakon cigaba da ruruwar annobar Coronavirus wanda a yanzu haka ya kama mutane 133.

A wani labarin kuma, karamin ministan harkokin kiwon lafiya, Adeleke Mamora ya bayyana cewa an samu wani likita dan Najeriya da ya rasa ransa a sakamakon annobar cutar Coronavirus a kasar Canada.

Minista Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake bayar da jawabi a kan cutar Coronavirus ga manema labaru inda yace sunan wannan likita dan Najeriya Olumide Okunuga.

“Ya kamata kowa ya zama mai lura da ankara, na ji jama’a na cewa wai bakar fata na da kariya daga cutar Coronavirus, wai ba za ta iya cutar damu ba, don haka nake shaida mana cewa bakar fata kuma dan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar.

“Mun samu labarin wani likita dan Najeriya dake zama a kasar Italiya wanda ya mutu a sakamakon cutar, don haka akwai bukatar mu yi taka tsantsan game da sauraron batutuwan da basu tabbata ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel