Bidiyo: An Hango Zarah, Ɗiyar Buhari Tana Rusa Kuka a London bayan Rasuwar Mahaifinta
- Iyalan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun shiga cikin bakin ciki bayan da aka tabbatar da rasuwarsa a asibitin London
- Wani faifan bidiyo ya nuna Zahra Buhari tana kuka a gaban asibitin, yayin da sauran ‘yan uwanta suka rike ta suna rarrashin ta
- An rahoto cewa tsofaffin shugabanni da jami’an gwamnati kamar Abdulsalami Abubakar da Rochas Okorocha sun ziyarci asibitin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
London - Iyalan tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari sun shiga cikin tsananin tashin hankali a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.
A ranar ne Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibitin London, inda aka ga dukkanin 'ya'yansa da matarsa Aisha Buhari a wajen asibitin.

Source: Twitter
Bidiyon Zahra Buhari tana kuka a London
Wani bidiyo da Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X, an hango Zahra Buhari ta fito daga cikin asibitin tana rusa kuka, saboda tsananin radadin mutuwar mahaifinta.

Kara karanta wannan
London Clinic: An gano makudan kudi da ake biya kullum a asibitin da Buhari ya rasu
Jim kadan sai aka ga sauran 'yan uwanta sun fito sun sameta, sun rirrike ta tare da shigar da ita cikin asibitin da mahaifin ya rasu.
Har Ila yau, bidiyon ya nuna lokacin da Aisha Buhari ta fito daga cikin asibitin, ta shiga wata mota, yayin da wasu 'yan uwansu ke binta a baya.
'Yan siyasa sun je asibitin da Buhari ya rasu
Channels TV ta rahoto cewa tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Abdulsalmi Abubakar da tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha suna asibitin yanzu haka.
Baya ga su, an ce akwai wani tsohon sakataren gwamnatin tarayya da shi ma ya ziyarci asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu a London.
Ganin wannan bidiyon ya raunana zukatan 'yan Najeriya, wadanda suke ci gaba da aika sakon ta'aziyya ga iyalan Buhari tun jiya Lahadi da aka sanar da rasuwarsa.
Kalli bidiyon a nan kasa:

Source: Twitter
Mutane sun yi martani kan bidiyon Zahra
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyi jama'a game da wannan bidiyo:
@FrolanMedia:
"Wannan bidiyon yana da matuƙar taɓa zuciya. Ina iya hango irin raɗaɗin da suke ciki. Ina addu'ar ubangiji ya ba su ƙarfin zuciyar haƙuri da wannan rashi."
@DbPragmatic:
"Rasuwar uwa ko uba abu ne mai matuƙar tayar da hankali.
"Allah ya ba Zahra, dukkan ’ya’yansa, da uwargida Aisha Buhari haƙurin wannan rashi, inda miƙa saƙon ta’aziya ta gare su."
@haassaan___:
"Zahra kamar mu take. Allah ya jiƙan Baba Buhari, ya yi masa Rahama. Ameen."
@Chisomstanley8:
"Ina addu’ar Allah maɗaukaki ya bai wa danginsa ƙarfin gwiwa su jure wannan babban rashi."
@SaidiBienvenu:
"Ba abu ne mai sauƙi ba… rasa masoyi, musamman uba ko uwa, abin na da matuƙar raɗaɗi."
@Nb_Ab_:
"Yanzu shi kenan mutane ba za su iya yin makoki cikin natsuwa ba; dole sai rayuwarsu ta sirri ta bayyana a kafafen sada zumunta."
Legit Hausa ta ji ta bakin mutane
Legit Hausa ta tattauna da mutane daban daban bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar:
Hajara Umar Muhammad daga Funtua ta ce ta kadu matuka da ta ji cewa Buhari ya rasu, tana mai cewa:
"Gaskiya mutuwarsa ta girgiza ni. Mutuwar sanannen mutum kamarsa, dole ta girgiza ka, sai ka dauka kamar ma ba da gaske ba ne, to amma an san mutuwa ba a yi mata wasa.
"Ina rokon Allah ya jikansa da Rahama, ya gafarta masa kura-kuransa. Ni dai, duk abin da ya yi mun na yafe, ba zan so a tsayar da mu gaban Allah ana yi mana hisabi ba. Kowane shugaba yana da dai dai yana da kuskure."
Mista Markus Danladi daga jihar Bauchi kuwa cewa ya yi:
"Oga Sani, ka san da ka fada mun ban yarda ba, sai da na duba na tabbatar, ba don ban yarda da kai ba, amma labarin ya zo kamar almara.
"Ubangiji ya karbe shi. Ubangiji ya ba shi salama a kabarinsa. Ina ta'aziyya ga iyalansa da mu 'yan kasa baki daya."
Hauwa Jidda Aliyu daga jihar Yola ta ce:
"Allah ya jikansa da Rahama. Ya yi mulki ya gama, Allah ya ba shi ikon amsa tambayoyin kabari. Allah ya sa shugabanni su dauki wa'azi daga mutuwarsa."

Kara karanta wannan
An gano bidiyon Aisha Buhari tana rusa kuka a gaban Shettima yayin da ya ke ta'aziyya
Tinubu ya dauki matakai bayan rasuwar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Shugaba Bola Tinubu ya dauki wasu muhimman matakai biyar.
Daga cikin matakan da ya dauka akwai umarnin saukar da tutoci na kwanaki bakwai da kuma tura Kashim Shettima zuwa Birtaniya don rako gawar Buhari.
Legit Hausa ta yi nazari kan matakai guda biyar da Shugaba Tinubu ya ɗauka don karrama tsohon shugaban ƙasar da ya rasu yana da shekara 82.
Asali: Legit.ng
