Trump Ya Girgiza da Masifar da Ta Tunkari Amurka, Najeriya Ta Yi Jaje

Trump Ya Girgiza da Masifar da Ta Tunkari Amurka, Najeriya Ta Yi Jaje

  • Gwamnatin Najeriya ta jajanta wa gwamnatin Amurka kan ambaliyar ruwa da ta hallaka mutum 120 a jihar Texas
  • Tuni Shugaba Donald Trump da uwargidansa Melania suka kai ziyarar ta’aziyya da duba barnar da ambaliyar ta jawo
  • Najeriya ta fitar da sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ta, tana mika sakon ta’aziyya da fatan samun sauki kan lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana alhini da jimamin ta kan ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Texas da ke Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutum 120 tare da barin fiye da 160 da ba a san inda suke ba.

Yadda ambalia ta yi barna a Amurka
Yadda ambalia ta yi barna a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ne ya wallafa sakon ta'aziyyar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kotu ta nemi a cafke Hamdiyya Sidi da ta 'ci mutuncin' gwamnan Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuggar ya ce Najeriya ta nuna matukar bakin ciki da wannan mummunar masifa, tare da mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin Amurka da al’ummar ƙasar gabaɗaya.

Najeriya ta ce tana addu’a ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata ko suka rasa dukiyoyinsu.

Trump ya kai ziyarar gani da ido wajen

A karshen mako, Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania sun ziyarci yankunan da ambaliya ta shafa a tsakiyar Texas.

BBC ta wallafa cewa yayin wata ganawa da jami’an gaggawa da na gwamnatin jihar, Trump ya bayyana cewa bai taɓa ganin irin wannan barna ba a rayuwarsa.

Bincike na ci gaba da nuna cewa wasu al’ummomi ba su samu gargaɗin isowar ambaliyar cikin lokaci ba, abin da ya sa ake zargin hukumomi da gazawa wajen dakile hasarar rayuka.

Ambaliya ta lalata gidaje da hanyoyin Amurka

Kara karanta wannan

Amurka ta yi wa Najeriya martani bayan kin karbar 'yan ciranin da Trump zai turo

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ta zo da ƙarfi bayan ruwan sama da ya sauka fiye da yadda ake tsammani, har ya haifar da cikar koguna da ambaliya a manyan birane da ƙauyuka.

Gidaje da dama sun nutse, hanyoyi sun lalace, da dama daga cikin abubuwan hawa sun bace. Jami’an ceto na ci gaba da kokarin gano waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Najeriya yi wa Amurka jaje da addu’a

Najeriya ta bayyana cewa tana tare da Amurka a wannan lokaci na jarrabawa. Ta jaddada cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu na da tushe mai ƙarfi, kuma za ta ci gaba da kasancewa.

Fiye da mutane 12,300 ne ke aikin ceto a halin yanzu a Texas, a cewar shugaban hukumar gaggawa ta jihar, Nim Kidd.

Najeriya ta ki karbar 'yan ciranin Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da bukatar Donald Trump na karbar 'yan ciranin Amurka.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ne ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi da manema labarai a makon da ya wuce.

Yusuf Tuggar ya bayyana cewa Najeriya tana fama da matsalolin karan kanta saboda haka ba za ta iya daukar karin matsaloli ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng