"Yan Jarida 12 Sun Mutu," Iran Ta Sake Kwance Wa Isra'ila Zani a Kasuwa bayan Yaƙi
- Isra'ila ta kashe ƴan jarida 12 a tsawon kwanaki 12 da aka yi ana musayar wuta tsakaninsa da Iran a watan Yuni
- Hukumomin kasar Iran sun ce waɗannan ƴan jarida da ma'aikatan kafafen watsa labarai sun rasa rayukansu ne a hare-haren Isra'ila
- Iran ta zargi Isra'ila ta kai hare-hare kan gidajen yaɗa labarai domin dakile gaskiya da hana masu adawa da ita motsi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Ƙasar Iran ta ƙara fallasa kisan da Isra'ila ta yi wa ƴan jarida, waɗanda a dokar yaki, ba a taɓa su, a lokacin rikicin ƙasashen biyu wanda ya shafe kwanaki 12.
Iran ta ce akalla 'yan jarida da ma'aikatan kafafen yaɗa labarai 12 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai yayin yakin da ya gudana kwanan nan tsakanin kasashen biyu.

Kara karanta wannan
Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

Source: Twitter
Gidan talabijin na gwamnatin ƙasar Iran ne ya tabbatar da alƙaluman a yau Alhamis, 10 ga watan Yuli, 2025, jaridar Arab News ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isra'ila ta kashe ƴan jarida 12 a Iran
Hukumar yaɗa labarai ta rundunar Basij, reshe ne na Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC), ta bayyana cewa adadin ƴan jaridar da suka mutu ya kai 12.
Ta ce adadin ya kai haka ne bayan gano wasu ƙarin mutane biyu da suka rasa rayukansu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA ya ruwaito.
Hukumomin Iran sun zargi Isra’ila da kai hare-haren da gangan kan cibiyoyin yaɗa labarai da nufin “dakile muryar gaskiya” da kuma murkushe “kafafen watsa labarai na ƴan wagwarmaya."
Alƙaluman rasa rayuka sun karu a Iran
Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda suka mutu a yaƙin Iran da Isra'ila ke ƙaruwa, duk da an tsagaita wuta bayan kwana 12.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027
An fara wannan yaƙi ne a ranar 13 ga Yuni da wani mummunan harin ba zata da Isra'ila ta kai Iran, wanda ya yi ajalin manyan sojoji da fararen hula.
Isra'ila dai ta yi luguden wuta kan muhimman wurare a Iran ciki har da sansanonin sojoji, wuraren nukiliya da yankunan zama a jamhuriyar musulunci.

Source: Getty Images
Yadda Isra'ila ta farmaki ƴan jarida
A lokacin rikicin, Isra’ila ta kuma kai hari a kan gidan rediyo da talabijin na gwamnati da ke Arewacin Tehran, rahoton Vanguard.
Wannan mataki na Isra’ila ya kashe manyan kwamandojin soja, masana kimiyyar nukiliya da daruruwan fararen hula, inda adadin rayukan da aka rasa suka kai 1,060.
A gefe guda kuma, Iran ta mayar da martani da jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami, wanda ya kashe akalla mutane 28 a Isra’ila.
Iran ta gargaɗi Amurka kan kara kai hari
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta ja kunnen Amurka da kar ta kara kai mata hari idan tana a koma teburin tattaunawa kan shirinta na makamin nukiliya.
Amurka da Iran sun fara tattaunawa kan shirin nukiliyan Iran ne kafin Isra’ila ta kai hari kan wuraren nukiliya da cibiyoyin soja na Iran.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Majid Takht-Ravanchi, ya bayyana cewa dole ne Amurka ta daina shirin kai karin hare-hare a Iran.
Asali: Legit.ng