Trump Ya Faɗi Yadda Ya Kare Khamenei daga Mutuwar Wulakanci a Yaƙin Iran da Isra'ila

Trump Ya Faɗi Yadda Ya Kare Khamenei daga Mutuwar Wulakanci a Yaƙin Iran da Isra'ila

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya fadi yadda ya kare rayuwar jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei na Iran
  • Donald Trump ya zargi Khamenei da rashin godiya inda ya ce ya hana a hallaka jagoran addini na kasar Iran
  • Trump ya ce zai sake kai hari kan Iran muddin ta cigaba da kokarin mallakar makaman nukiliya, yana kuma kalubalantar maganganun Khamenei na nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma yin magana kan yakin da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila.

Shugaban kasar ya ce ya hana kashe Ayatollah Ali Khamenei na Iran, yana kuma sukar jagoran na Shi'a da rashin godiya.

Trump ya zargi Khamenei da ƙarairayi
Trump ya ce shi ya ƙare Khamenei daga mutuwa a yaƙi. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wani rubutu na musamman a Truth Social da Trump ya yi a yau Juma'a 27 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton France 24.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi yadda ta shirya kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Khamenei

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yaki ya daidaita Iran da Isra'ila

Wannan kalamai na Trump na zuwa ne bayan shafe kwana 12 ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Iran wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Fadan ta kara tsami ne bayan Donald Trump ya shiga yakin inda ya umarci kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Har ila yau, Trump ya bukaci zaman sulhu domin kawo karshen yakin inda gargadi kowane ɓangare da su mutunta kokarin tsagaita wuta.

Trump ya yi barazanar sake kai hari Iran

Trump ya ce zai umarci kara kai hare-hare idan Iran ta ci gaba da neman makaman nukiliya, yana dora laifi kan Khamenei saboda rashin jinjina.

Ya soki Iran saboda ikirarin nasara a yakin da ta yi da Isra’ila, yana janye sassaucin takunkumi.

Shugaba Trump ya ce Amurka za ta sake kai hari ba tare da wata shakka ba idan Iran ta ci gaba da tace uraniyum din makaman nukiliya duk da hare-haren da aka kai.

Kara karanta wannan

Jerin ƙasashen da suka mallaki makamin nukiliya a duniya da adadinsu

Trump ya sha alwashin sake kai hari Iran
Trump ya bukaci Khamenei ya yi masa godiya. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Trump ya zargi Khamenei da ƙarairayi

Shugaban Amurka ya zargi Khamenei da rashin godiya bayan ya ce harin da aka kai wa wuraren nukiliyarsu bai yi wata illa ba.

Trump ya rubuta:

“Na san daidai inda yake boye, amma ban bar Isra’ila ko Sojojin Amurka sun kashe shi ba.
“Ina ce: na ceto shi daga mutuwar wulakanci, kuma bai ce: ‘na gode, shugaba Trump!’ ba."

- Cewar Donald Trump

Trump ya ce yana kokarin cire takunkumi kan Iran, wanda ke cikin bukatunsu tun da dadewa, amma ya dakatar bayan irin kalaman Khamenei, The Hill ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Maimakon godiya, sai na samu fushi da kyama, hakan yasa na dakatar da komai game da sassaucin takunkumi."

Iran tana bincike kan barna a cibiyoyin nukiliyarta

Mun ba ku labarin cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce yaki da Isra’ila ya jawo mummunar barna a cibiyoyin nukiliyar kasar.

Kara karanta wannan

'Mun shirya': Khamenei ya gargadi Amurka da Isra'ila, ya ce komai na iya faruwa a gaba

Araghchi ya bayyana cewa masana daga Hukumar Makaman Nukiliya ta Iran na binciken hasarar tare da shirya neman diyyar barnar da aka yi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da sojojin kasarsa suka kai sun lalata cibiyoyin nukiliya don taimakawa Isra’ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.