Iran Ta Faɗi Gaskiya kan Illar da Hare Haren Isra'ila Suka Yi Wa Cibiyoyin Nukiliyarta
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce yaki da Isra’ila ya jawo mummunar barna a cibiyoyin nukiliyar kasar
- Araghchi ya bayyana cewa masana daga Hukumar Makaman Nukiliya ta Iran na binciken hasarar tare da shirya neman diyyar barnar da aka yi
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai sun "lalata" cibiyoyin nukiliya don taimakawa Isra’ila
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi magana kan barnar da hare-haren Isra'ila suka yi musu.
Araghchi ya fada a ranar Alhamis cewa suna ci gaba da bincike kan barnar da aka yi wa cibiyoyin nukiliya yayin yaƙin da aka yi.

Source: Getty Images
Iran na tattara bayanai kan cibiyoyin nukiliyarta
Rahoton India Today ya ce ministan ya fadi haka ne yayin da kasar ke fara tantance tasirin barnar a Iran a yaƙin kwana 12 da Isra’ila wanda ya kasance “mai tsanani”.
Ya ce masana daga hukumomin makaman nukiliya suna aiki ba dare ba rana domin bincike kan lamarin.
Ya ce:
“Masana daga Hukumar Makaman Nukiliya (na Iran) na gudanar da cikakken bincike kan barnar da aka yi.
“Yanzu, batun neman diyyar wannan barna da bukatar a biya ya shiga cikin manyan batutuwa a ajandar diflomasiyyar kasar.
“Wannan barna mai tsanani ce, kuma binciken masana da yanke shawara a fannin siyasa na gudana a lokaci guda.”

Source: Getty Images
Hari kan nukiliya: Iran ta fasa ganawa da Amurka
Dalilin haka, ministan ya ce Iran ba ta da wani shiri na ganawa da Amurka a makon gobe.
Yayin da yake ganawa da yan jaridu a ranar Alhamis, Araghchi ya karyata ikirarin Shugaba Donald Trump cewa za a yi ganawar mako mai zuwa.
Araghchi ya ce Tehran na ci gaba da tantance ko sake shiga tattaunawa da Washington zai amfani kasar.
Ya ce hakan na da muhimmanci ganin cewa an katse zaman tattaunawa guda biyar da suka gabata sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran.
Abin da Trump ya ce kan nukiliyar Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha nanata cewa hare-haren sama da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran sun yi barna.
Shugaba Trump ya ce an yi hakan ne domin taimakawa abokiyarta watau kasar Isra’ila saboda lalata wuraren, Vanguard ta ruwaito.
An yi ta samun rahotanni mabanbanta kan harin da Amurka ta kai inda wasu ke cewa babu abin da ya samu cibiyoyin nukiliyar Iran.
Benjamin Netanyahu zai fuskanci tuhuma a Isra'ila
A baya, kun ji cewa kwana 2 da kammala yaƙi da Iran, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanayahu zai fuskanci shari'a kan zarge-zargen rashawa.
An ce Netanyahu ya roki kotu ta taimaka da ɗage wannan shari'a duba da yanayin da ƙasar ke ciki na yaƙi da kungiyar Hamas da ke Gaza.
Hakan ya biyo bayan maganar Shugaban Amurka, Donald Trump inda ya bukaci a dakatar da wannan shari'a ko kuma a yi wa Netanyahu afuwa.
Asali: Legit.ng

