Iran, China da Rasha Sun Yi Taro yayin da Trump Suka Hadu a Netherlands
- Kasar China ta gudanar da taron ministocin tsaro na ƙasashe mambobin ƙungiyar SCO a birnin Qingdao
- Ministocin tsaro daga Iran da Rasha sun tattauna a lokacin da rikici ke gudana a Gabas ta Tsakiya da kuma zaman NATO a Turai
- China ta bayyana taron a matsayin hanyar ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a duniyar yau mai cike da rudani
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
China - Kasar China ta karɓi ministocin tsaro daga Iran da Rasha a birnin Qingdao da ke gabashin ƙasar, inda aka gudanar da taron manyan jami’an tsaro na ƙungiyar SCO.
Wannan taro ya zo a daidai lokacin da ake fama da rikici a Gabas ta Tsakiya da kuma ci gaba da zaman shugabannin ƙasashen NATO a Turai.

Source: Getty Images
Tashar France 24 ta wallafa cewa taron ya gudana ne yayin da aka tsagaita bayan yaki tsakanin Iran da Isra’ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta rahoto cewa an shafe kwanaki 12 ana gwabza yaki tsakanin Iran da Isra’ila kafin samun yarjejeniyar zaman lafiya.
A lokaci guda, ƙasashen NATO na ƙoƙarin ƙara yawan kasafin kudi a fannin tsaro, musamman don biyan buƙatar Amurka.
China da Rasha magantu da matsalolin duniya
Ministan tsaro na Rasha, Andrei Belousov, ya bayyana halin da duniya ke ciki a matsayin mai muni da cike da rudani.
A cewarsa, rikice-rikicen siyasa da soja sun ƙaru fiye da da, inda ya buƙaci haɗin kai a tsakanin ƙasashen SCO don tinkarar kalubalen.
Shi ma ministan tsaron China ya bayyana muhimmancin taron na Qingdao da ke cike da alaka da sansanin jiragen ruwa na ƙasar.
Ya ce duniya na fama da rudani da sauye-sauye masu hadari, kuma lokaci ya yi da SCO za ta taka rawar gani wajen tabbatar da kwanciyar hankali.
An tattauna batun Iran da Amurka a taron
Yayin taron, an yi hasashen cewa batun rikicin da ya shafi Iran, Isra’ila da Amurka ya kasance cikin abubuwan da aka tattauna.
Duk da kasancewar Iran abokiyar China, Beijing ta takaita kan bayar da goyon bayan diflomasiyya kawai, don guje wa rikici da Washington.

Source: Getty Images
India ta yi kira ga haɗin kai a duniya
Rahoton Times of India ya nuna cewa ministan tsaron India, Rajnath Singh, wanda shi ma ya halarci taron, ya bukaci mambobin SCO su haɗa kai wajen fuskantar kalubalen duniya.
Ya bayyana yadda duniya ke fuskantar sauye-sauyen tattalin arziki da siyasa, yana mai cewa lokaci ya yi da ƙasashen SCO za su tsaya tsayin daka wajen kare muradun jama’arsu.
Kwamandan Iran ya bayyana bayan 'kashe' shi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban sojin Iran Esmail Qaani ya bayyana a bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi.
Kasar Isra'ila ta ce ta kashe shugaban sojin ne a wani hari da ta kai Tehran yayin da suke tsaka da yaki da Iran.
Legit Hausa ta gano cewa shugaban sojojin ya bayyana ne a wani taron gangami da Iran ta yi domin nuna cewa ta yi nasara a yaki da Isra'ila.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

