Sabuwar Matsala: Isra'ila za Ta Gurfanar da Netanyahu, Trump Ya Nemi Afuwa
- Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci a soke shari’ar rashawa da ake yi wa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu
- Trump ya bayyana Netanyahu a matsayin gwarzon Isra'ila, yana mai cewa Amurka za ta “cece shi kamar yadda ta ceci Isra’ila.”
- Shari’ar da ke kan Benjamin Netanyahu ta shafi tuhuma uku da suka hada da cin hanci, almundahana da cin amanar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bukaci a soke shari’ar rashawa da ake yi wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Idan ba za a soke shari'ar ba, Trump ya nemi a masa afuwa, yana mai bayyana Netanyahu a matsayin “gwarzo” da ya yi wa ƙasarsa aiki tukuru.

Source: UGC
Rahoton Reuters ya ce Trump ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yana mai cewa “Amurka ta ceci Isra’ila, kuma yanzu za ta ceci Netanyahu.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuhume tuhume 3 da ake yi wa Netanyahu
Netanyahu da ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, na fuskantar tuhuma uku da suka shafi cin hanci, karkatar da kudi da kuma amfani da ofis din gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Rahoton Al-Jazeera ya tabbatar da cewa an fara sauraron shari’ar ne a 2020, bayan an gurfanar da shi a 2019.
Kamar yadda rahotannin kafafen watsa labaran Isra’ila suka bayyana, an fara tambayarsa a kotu a ranar 3 ga Yuni, 2025, kuma ana sa ran tambayoyin za su dauki sama da shekara guda.
Sai dai Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, wanda ke da ikon yin afuwa, ya bayyana cewa ba a kawo masa wata bukata ta afuwa daga Netanyahu ba.
Trump ya soki batun gurfanar da Netanyahu
Trump ya bayyana shari’ar da ake yi wa Netanyahu a matsayin “bita da kulli,” yana mai kwatanta ta da shari’o’in da aka yi masa a Amurka dangane da harkokin siyasa.
A cewarsa:
“Bibi Netanyahu ya yi abubuwa da dama saboda Isra’ila. Ya kamata a kawo karshen wannan shari’ar da ake yi masa nan take.”
Sai dai har yanzu ba a fayyace ko Trump yana da wata hanya ta doka da zai iya amfani da ita domin dakatar da shari’ar Netanyahu ba.
Amma bayyana goyon bayansa da ya yi a fili na iya ƙara hura wutar ce-ce-ku-ce a tsakaninsa da wasu shugabannin duniya.

Source: Getty Images
Trump na wannan furuci ne yayin da yake halartar taron koli na NATO a ƙasar Netherlands, inda ake sa ran zai ci gaba da bayyana matsayinsa kan rikicin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya ce Iran ta ragargaji Isra'ila
A wani rahoton, kunj ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya yi sharhi kan yakin da aka shafe kwana 12 ana yi tsakanin Iran da Isra'ila.
Shugaban Amurka ya ce babu shakka Iran ta yi wa Isra'ila ba dadi musamma a kwanakin karshe na yakin.
A bayanin da ya yi, Donald Trump ya ce akwai yiwuwar Amurka ta sake kulla alaka da Iran a shekaru masu zuwa.
Asali: Legit.ng

