Gaza: An Gano Yadda Mutane 870 Suka Mutu a Kwanaki 12 na Yaƙin Iran da Isra'ila
- Isra'ila ta yi amfani da yadda hankalin duniya ya koma kan faɗanta da Iran, ta kashe falasɗinawa 870 a tsawon kwanaki 12
- Ma'aikatar Lafita ta Gaza ta bayyana cewa a kusan mako biyu da aka yi ana musayar wuta tsakanin ƙassahen biyu, Isra'ila ta halaka mutane da yawa
- Tuni dai ƙasashen duniya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka yi Allah wadai da ta'addancin da Isra'ila ke aikatawa a Gaza
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gaza - A daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata kan yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran, ƙasar yahudawa ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin Isra'ila sun ci gaba da kai hari a Gaza, lamarin da ya janyo asarar rayukan daruruwan falasɗinawa cikin kwanaki 12.

Kara karanta wannan
Rufa rufa ta ƙare: An gano mummunan halin da Iran ta jefa Isra'ila bayan tsagaita wuta

Source: Getty Images
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa akalla falasɗinawa 870 ne suka rasa rayukansu a hannun dakarun Isra’ila a kwanaki 12 da Isra’ila ta yi tana faɗa da Iran, cewar rahoton Al-Jazeera.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe sun haura 56,000
Wannan na zuwa ne a lokacin da musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu ya janyo damuwa a fadin duniya, musamman saboda fargabar yaɗuwar yaƙin.
Sakamakon haka, jimillar Falasɗinawan da suka mutu tun farkon yaƙin da Isra’ila ke yi da ƙungiyar Hamas daga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, ya kai mutum 56,077.
An tattaro cewa wannan alƙaluman na waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu kuma aka ga gawarsu ne, ban da waɗanda gini ya faɗo kansu da ba a iya ciro gawarsu ba.
Mutanen Gaza na bukatar agajin duniya
Masu aikin jin ƙai sun bayyana cewa Gaza tana fuskantar babban bala’i kuma galasɗinawa na buƙatar da tallafin jin-ƙai, rahoton BBC News.
Dama tun kafin harin da Isra’ila ta fara kai wa Gaza, yankin na fama da yunwa, rashin ruwa da magunguna, da kuma lalacewar cibiyoyin lafiya da ilimi.
Har yanzu dai ana ci gaba da hana yankin samun duk wani taimako daga waje, inda ake cewa ba a bari kayan agaji su shiga cikin Gaza yadda ya kamata duk da matsin lamba daga ƙasashen duniya.

Source: Getty Images
Isra'ila ta durar wa Gaza ana yakin Iran
A yayin da duniya ta fi mayar da hankali kan yaƙin Iran da Isra’ila, an yi biris da yadda Isra’ila ke amfani da wannan dama wajen ƙara tsananta farmaki a Gaza.
Masu rajin kare hakkin bil’adama sun bayyana damuwarsu cewa Isra’ila na amfani da rikicinta da Iran wajen karkatar da hankalin duniya daga ta’addancin da take yi a Gaza.
Ƙasashe da dama, ciki har da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na agaji da kare haƙƙin dan Adam, sun ƙara matsa lamba ga Isra’ila da ta dakatar da kai hare-haren da ke ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.
Halin da Isra'ila ta shiga bayan yaƙin Iran

Kara karanta wannan
Wace ƙasa ta yi nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu ya yi jawabi bayan tsagaita wuta
A wani rahoton, kun ji cewa Isra'ila ta faɗa matsin tattalin arziki sakamakon ɓarnar da Iran ta yi mata a tsawon kwanaki 12 ƙasashen biyu suka yi musayar wuta.
Rahotanni daga masana da kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa biliyoyin Daloli ne suka salwanta sakamakon wannan rikici.
Wani masani, Naser Abdelkarim ya ce Iran ta yi wa Isra'ila mummunar illa kuma ba a ɓangaren tsaro kaɗai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng