Trump Ya Yi Tonon Silili a Taron NATO, Ya Ce Isra'ila Ta Sha Wuta a Hannun Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da sojojin Amurka suka kai sun rushe cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya
- Ya bayyana hakan ne a taron shugabannin NATO da ke gudana a Netherlands, inda ya ce tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila na tafiya daidai
- Trump ya ce Iran ta harba manyan makamai da suka yi illa a kasar Isra'ila yayin da suka shafe kwanaki 12 suna gwabza yaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Netherlands - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran ya haifar da “cikakken rusau.”
Ya fadi haka ne duk da cewa rahoton sirri ya nuna cewa hare-haren sun jinkirta shirin Iran na ƙirƙirar makaman nukiliya ne na ‘yan watanni kacal.

Source: Twitter
TRT ta wallafa cewa Trump ya bayyana haka ne a taron shugabannin ƙasashen NATO da ke gudana a Netherlands.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump: An kai hare hare a Isra'ila
Shugaba Donald Trump bayyana cewa makamai masu linzami da Iran ta harba sun ragargaji Isra'ila sosai musamman a kwanakin karshe na yakin.
Baya ga haka, Trump ya bayyana cewa za su iya kulla alaka da Iran a gaba a wani bidiyo da tashar labaran ta wallafa a Facebook.
Trump ya kare matakin Amurka a taron NATO
Trump ya jaddada cewa ba za su taɓa yarda Iran ta ci gaba da haɓaka makamashin nukiliya ba, yana mai cewa an rage wa Iran damar sake kokarin hakan “na tsawon shekaru masu yawa.”
Shugaba Trump ya ce:
“Mun harba makamai masu linzami 30, kuma mun tarwatsa wuraren da Isra’ila ba ta kaiwa hari ba.”
Ya ce wannan mataki ne da ya kawo tsaiko sosai ga burin Iran, kuma hakan ya nuna karfin Amurka da aniyar kare Isra’ila.
Duk da cewa rahoton sirri ya nuna cewa Iran za ta iya dawowa da shirin nata cikin ‘yan watanni, Trump ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa:
“Ba zan ce kamar Hiroshima ba ko Nagasaki, amma wannan shi ne abin da ya kawo ƙarshen wancan yakin. Muna son a san cewa wannan hari ne na ƙarshe.”
Barazanar ficewa daga yarjejeniyar nukiliya
Rahotanni daga Tehran sun nuna cewa Iran na tunanin ficewa daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makamashin nukiliya (NPT) domin nuna rashin jin daɗi game da hare-haren Isra’ila da Amurka.
Trump dai ya ce yana ganin ana samun ci gaba a yakin Isra’ila da Hamas a Gaza, yana danganta hakan da tasirin harin da Amurka ta kai wa Iran.

Source: Getty Images
CNN ta wallafa cewa Trump ya ce:
“Na yi imani da cewa wannan hari da muka kai zai kawo cigaba wajen dakile Hamas. Ya nuna karfinmu,”
Kwamandan Iran ya bayyana bayan 'kashe' shi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban rundunar Amurka, Esmail Qaani ya bayyana a idon duniya bayan kammala yakin Iran da Isra'ila.
Shugaban sojojin ya bayyana ne a wani gangami da 'yan Iran suka shirya bayan tsagaita wuta a yakin da suka yi na kwana 12.
A wani hari da Isra'ila ta kai Iran ne ta bayyana cewa ta kashe Esmail Qaani wanda rashin ganin shi a zahiri ya jawo ce-ce-ku-ce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


