Abu Ya Girma: Iran Ta Kara Yunƙurowa Tun da Asubah, Ta Yi Ɓarin Wuta kan Isra'ila

Abu Ya Girma: Iran Ta Kara Yunƙurowa Tun da Asubah, Ta Yi Ɓarin Wuta kan Isra'ila

  • Da safiyar yau Asabar, Iran ta ci gaba da ɓarin wuta kan Isra'ila yayin da yakin da ya ɓarke tsakanin kashen biyun ke ƙara ta'azzara
  • Rahotanni sun nuna cewa Iran ta harba makami mai linzami yankin Holon a birnin Tel Aviv, inda aka hango gobara da hayaƙi na tashi
  • Sai dai Isra'ila ta maida martani da harba makamai a yankin Isfahan, inda ɗaya daga cikin cibiyoyin nukiliyar kasar Iran take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Rahotanni daga birnin Tel Aviv sun tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami zuwa wasu sassan Isra’ila da sanyin safiyar yau Asabar, 21 ga watan Yuni.

Daga cikin yankunan da Iran ta yi wa ɓarin wuta a Isra'ila a wannan rana har da unguwar Holon, inda aka hangi gobara da hayaki na tashi.

Kara karanta wannan

Yaƙin Iran da Isra'ila ya kawo hargitsi a taron UN, jakadu 2 sun yi musayar baƙaƙen kalamai

A shiga rana ta 8 a yakin Iran da Isra'ila.
Iran da Isra'ila sun ci gaba da musayar wuta tun da asubahin Asabar Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

A martanin da ta mayar, Isra’ila ta kai farmaki a Isfahan, wadda ke ɗauke da cibiyar binciken nukiliyar Iran, da kuma wasu yankuna daban-daban, rahoton DW Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe yaƙin Isra'ila da Iran zai zo ƙarshe?

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa wannan rikicin na iya ɗaukar lokaci mai tsawo, la'akari da yadda ƙasashen biyu ke kallon juna a matsayin abokan gaba.

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya bayyana cewa farmakin da ƙasarsu ta kai zai iya dakile burin Iran na kera makamin nukiliya har na tsawon shekaru biyu.

A ɓangaren Iran kuma, hukumomin tsaro sun ce tun daga 13 ga watan Yuni, sun kama mutum 22 a lardin Qom, bisa zargin suna yi wa Isra’ila leƙen asiri.

Ministan Iran ya tafi taro a Istambul

A gefe guda, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin Istanbul na Turkiyya a yau Asabar, domin halartar wani taro da ƙasashen Larabawa suka shirya.

Kara karanta wannan

Iran ta jefa yahudawa sama da 8,000 cikin mawuyacin hali da ta kai kare hare kan Isra'ila

Bayanai sun nuna cewa an shirya wannan muhimmin taro ne kan rikicin da ke ƙara zafi tsakanin Iran da Isra’ila.

Rahotanni sun ce ana sa ran jakadun diflomasiyya kusan 40 za su halarci taron a ƙarshen mako, wanda aka shirya bisa kiran Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi (OIC).

Iran ta ci gaba da kai hare-hare Isra'ila.
Ministan harkonin wajen Iran ya isa Istanbul don halartar taro Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Rikicin Iran da Isra'ila na ƙara tsanani

Wannan taro yana zuwa ne kwanaki bayan ganawar Araghchi da ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa da Jamus a birnin Geneva.

Isra’ila dai ta fara kai hare-haren ne a ranq 13 ga Yuni, tana zargin Iran da ƙoƙarin mallakar makaman nukiliya, zargin da Iran ta ce ba shi da tushe kuma ƙarya ce tsagwaronta.

Tun daga wannan lokaci, Iran ke ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya, wanda a yau Asabar ta sake kai farmaki kan ƙasar Isra'ila.

An kashe sama da mutane 600 a Iran

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar HRANA da ke Amurka ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe sama da mutum 650 a hare-haren da ta kai Iran a mako guda.

Kara karanta wannan

Isra'ila: Iran ta turje, ta yi fatali da zama a teburin tattauna wa da Amurka

HRANA ta fitar da sanarwa cewa mutane 657 ne aka tabbatar sun mutu, sannan wasu 2,037 sun jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Iran.

Ƙungiyar ta ce tana samun bayanai ne daga wani wasu masu ba ta rahoto daga cikin kasar Iran, da kuma bayanan da ke fitowa fili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel