Da Gaske Jirgin Mahajjattan Murtaniya Ya Fada Tekun Maliya, Alhazai Sun Mutu?

Da Gaske Jirgin Mahajjattan Murtaniya Ya Fada Tekun Maliya, Alhazai Sun Mutu?

  • Gwamnatin Mauritaniya ta karyata rade-radin da ke yawo cewa jirgin alhazanta ya yi hadari a gabar Tekun Maliya
  • Hukumomin Hajji na kasar sun tabbatar da cewa dukkan alhazansu sun isa Saudiyya lafiya cikin tsari da kwanciyar hankali
  • Kamfanin jiragen sama na kasar Mauritaniya ya ce ya yi jigilar alhazan ta jirage uku ba tare da wani hadari ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Gwamnatin Mauritaniya ta bayyana cewa labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa wani jirgin dauke da alhazan kasar ya yi hadari ba gaskiya ba ne.

Labari ya karade kafafen sada zumunta cewa dukkan mahajjatan da jirgin saman kasar ya dauki sun fada Tekun Maliya sun mutu.

Mohamed Ould Ghazouani
Murtaniya ta musa cewa mahajjtanta sun yi hadari. Hoto: Getty Images|@MCGhazouani
Source: Instagram

Rahoton Express TV ya nuna cewa zancen ba gaskiya ba ne, kuma an bukaci mutane su rika tantance labaru kafin yada su.

Kara karanta wannan

Jiran shekara 3: Za a fara hukunta daliban Najeriya da aka kama da satar amsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, Jaridar Blue Print ta wallafa cewa shugaban hukumar Hajji na ma’aikatar harkokin addinin Musulunci na kasar, El Waly Taha ya karyata jita jitar.

El Waly Taha ya bayyana hcewa babu wani jirgin Hajji daga kasar da ya gamu da hadari, kuma dukkan alhazansu sun isa kasa mai tsarki lafiya.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke shirin kammala shirye-shiryen fara Hajjin bana na shekarar 2025.

An tabbatar da isar alhazan Murtaniya Makka

El Waly Taha ya ce sun tabbatar da isar da alhazan Mauritaniya cikin tsari ba tare da wata matsala ba.

Ya ce jami’ansu na bin diddigin jirage da kuma saukarsu tun daga tashar jirgin saman Nouakchott har zuwa kasa mai tsarki.

A nasa bangaren, kamfanin jirgin saman kasar Mauritaniya ya ce sun gudanar da jigilar alhazan cikin tsaro da kwanciyar hankali.

Baya ga haka, kamfanin jirgin saman kasar Mauritaniya ya ce sun yi amfani da jirage uku ba tare da an samu wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Mahajjaciyar Najeriya ta rasu a asibitin Makkah

Kamfanin ya kara da cewa dukkan jiragen da aka tsara domin daukar alhazan kasar sun kammala sauke nauyin su cikin nasara, kuma babu wani rahoton matsala ko jinkiri da aka samu.

Tekun maliya: Jita jitar hadarin jirgin Murtaniya

A makon nan ne wata jita-jita ta yadu a kafafen sada zumunta cewa wani jirgi daga Mauritaniya dauke da alhaza ya fadi a gabar Tekun Maliya.

Biyo bayan jita jitar, lamarin ya tayar da hankalin ‘yan uwa da dangi a gida da wajen kasar Murtaniya.

Sai dai wannan karin bayani daga hukumomin kasar da kamfanin jirgin saman ya kawo karshen rudani, tare da tabbatar da cewa babu wani hadari da ya auku.

Tekun Maliya
Jirgi na tafiya a cikin Tekun Maliya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tekun Maliya na kan hanya tsakanin nahiyoyin Afirka da Asiya, kuma yana daya daga cikin manyan hanyoyin ruwa da alhazai ke bi zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji.

Aikin Hajji a idon Musulmai

Aikin Hajji daya ne daga cikin ibadu mafi girma da Musulmi ke yi a rayuwarsu, kuma yana kawo farin ciki da cikar buri ga miliyoyin mutane daga sassan duniya.

Duk da wahalhalun da ke tattare da tafiyar; irin su gajiyar tafiya, cunkoso, zafi mai tsanani da kuma hadurran da ka iya faruwa, hakan bai hana Musulmi sha’awar zuwa wannan kasa mai tsarki ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

A lokuta da dama, ana samun rahotanni na mutane da suka rasa rayukansu yayin hajji saboda cinkoso ko yanayi, amma hakan ba ya rage darajar aikin a zukatan Musulmi.

Maƙasudin hajji da albarkar da ke cikinsa na ƙarfafa imani da haƙuri, wanda hakan ke sa jama’a ci gaba da zuwa kowace shekara, ko da da wuya.

Hukumar hajji ta kowace kasa kan dauki matakan tabbatar da lafiya da tsaron jama’a, inda ake yi musu horo da shiryawa kafin tafiya.

A gefe guda, hukumar kula da yanayi da zirga-zirga kamar su kamfanonin jiragen sama suna taka rawar gani wajen isar da alhazan cikin kwanciyar hankali.

Wannan ne ya sa ko da ake fuskantar kalubale, aikin hajji na ci gaba da zama tushen farin ciki, sabuwar rayuwa da kusantar Allah ga duk mai imani.

Mahajjaciyar Najeriya ta rasu a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa mahajjaciyar Najeriya, Adizatu Dazumi ta rasu a kasar Saudiyya bayan kammala dawafi.

Hukumar alhazan Najeriya reshen jihar Edo ta tabbatar da rasuwar Hajiya Adizatu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban hukumar alhazai ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayiyar bayan tabbatar da cewa an birne ta kamar yadda Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng