Trump Ya Yi Martani ga Najeriya, Ya Daga Harajin Shigar da Kaya Kasar Amurka

Trump Ya Yi Martani ga Najeriya, Ya Daga Harajin Shigar da Kaya Kasar Amurka

  • Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana rashin gamsuwa da yawan harajin da 'yan kasuwar suke biya
  • Najeriya ta ɗora harajin 27% a kan dukkanin kayayyakin da ake shigowa da su cikin ƙasar nan daga Amurka
  • Wannan lamari ya jawo Donald Trump ya yi martani, ya sanya Najeriya a kasashen da aka yi wa karin haraji karin haraji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa daga yanzu, za a sanya harajin 14% a kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka.

An sanar da wannan mataki ne a yayin wani taron kara wa Amurka arziki da aka gudanar a Rose Garden ranar Laraba, a wani mataki na daidaita tsarin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

Trump
Amurka ta kara yawan harajin shigo da kaya Amurka Hoto: @OfficialBAT/@Trump
Asali: Twitter

The Punch ta ruwaito cewa wannan sabon haraji na 14% yana nuna sauyi mai girma a dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa tana kokarin magance rashin daidaito a cinikayyar kasashen biyu, inda ta ce an dade ana cutar da kasar a wannan ɓangaren.

Dalilin harajin Amurka na a kan kayan Najeriya

Vanguard ta ruwaito cewa, a cewar gwamnatin Trump, Najeriya na kakabawa kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka haraji na 27%.

Gwamnatin Amurka ta ce wannan bambanci ya dade yana cutar da 'yan kasuwanta da kuma masu sayayya.

A matsayin martani, Amurka ta dauki matakin sanya haraji a kan kayan da Najeriya ke fitarwa domin rage abin da ta kira tsarin kasuwanci maras adalci.

A jawabin da ya gabatar, Trump ya bayyana cewa wannan haraji yana cikin wata babbar manufa ta kare masana'antun Amurka da tilasta wa kasashen waje bin ka'idojin ciniki na adalci.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Yadda Edwin Clark da fitattun ƴan siyasa 4 suka mutu a 2025

An dora Amurka kan sabon tsarin haraji

Trump ya bayyana cewa an shiga sabon zamani farkon wani sabon zamani na abin da ya kira ciniki na gaskiya da adalci.

Ya ce matakin zai karfafa masana’antu a Amurka da kuma tilasta wa kasashen waje bude kasuwanninsu da ake zargin sun daɗe suna hana kayayyakin Amurka shiga.

Ya ce:

“Wannan daya ne daga cikin manyan ranaku masu tarihi a Amurka.”
“Tabbas, wannan zai zama zamanin dawowar Amurkawa. Za mu dawo da karfinmu.”

Trump ya kuma bayyana sabuwar manufar kasuwanci da ta hada da harajin 10% a kan duk wani kaya da ake shigowa da shi zuwa Amurka.

Tsarin harajin Amurka ya fara aiki

Wannan sabon haraji ya fara aiki nan take, kuma yana shafar kasashe sama da 50, daga ciki har da China, Tarayyar Turai, Indiya da Japan, tare da kasashe masu tasowa a Asiya, Afirka da Kudancin Amurka.

Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Asali: Twitter

Sabuwar manufar kasuwancin ta kawo sauyi mai girma a fannin kasuwanci da tattalin arziki na duniya.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

Lamarin ya jefa ƙasashen duniya a cikin tashin hankali tare da haifar da fargabar barkewar yakin ciniki na duniya.

Kasuwar Dangote ta buɗe a Amurka

A baya, kun samu labarin cewa matatar mai ta Dangote ta ci gaba da shahara a kasuwannin duniya, inda ta fitar da man jirgin sama zuwa Amurka a watan Maris.

Haka kuma, matatar ta riga ta tura jiragen ruwa guda shida dauke da ganguna miliyan 1.7 na man jirgin sama zuwa Amurka yayin da ta ke harin kasuwannin Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.