"Azumi 29 ko 30?": An Yi Hasashen Ranar da Za a Yi Karamar Sallah a Saudiyya da Wasu Kasashe
- Saudiyya, Qatar da wasu kasashen duniya sun fara shirin duban jinjirin watan Shawwal ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan, 1446AH
- A addinin musulumci, kowane wata ya na yin kwanaki 29 ne amma idan ya ɓuya ko wani dalili da ya sa ba a gan shi ba, zai cika 30
- Masana sun bayyana cewa akwai damar ganin watan ƙaramar sallah ranar Asabar, amma kuma sun ce za ta iya yiwuwa a ƙi ganinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudiyya - Yayin da ake shirye-shiryen fara duban jinjirin watan Shawwal, na 10 a jerin watannin Musulunci, musulmai a faɗin duniya sun fara shirin sallah.
Ƙaramar sallah dai ita ke nuna musulmi sun kammala azumin watan Ramadan domin ana yin hawan idi ne ranar 1 ga watan Shawwal na kowace shekara.

Asali: Twitter
Jaridar Hindustan Times ta tattaro hasashen ranar da za a iya ganin jinjirin wata a ƙasashen Larabawa da ke Gabas ta Tsakiya da kasashen Yamma irinsu Amurka da Faransa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa tsarin kalandar Musulunci ana buƙatar duban wata domin tabbatar da ranar Eid-ul-Fitr.
Hasashen ranar sallah a Saudiyya da wasu kasashe
A kasashen Gabas ta Tsakiya irin su Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, da Kuwait, da kuma kasashen Yamma irin su Amurka, Birtaniya, Faransa, da Jamus, za a fara duban jinjirin wata ranar Asabar.
Hukumomin kasashen da ma wasu da dama za su fara duban jinjirin watan Shawwal bayan sallar Maghrib a daren 29 ga Ramadan 1446 AH, wanda ya yi daidai da 29 ga Maris, 2025.
Idan Allah ya sa aka ga jinjirin watan Shawwal a wannan dare, to za a gudanar da Eid-ul-Fitr a ranar 30 ga Maris, 2025.
Idan kuwa ba a ga watan ba a wannan rana, Ramadan zai cika kwanaki 30, kuma za a yi Sallah a ranar 31 ga Maris, 2025 daidai da 1 ga watan Shawwal, 1446H.

Kara karanta wannan
Mutane sun ga abin al'ajabi da wani bawan Allah ya rasu a masallaci bayan sallar asuba
Za a iya ganin watan Shawwal ranar Asabar?
Masana sun bayyana cewa da yiwuwar a ga jinjirin watan ranar Asabar, amma dai zai fi fitowa ranar Lahadi, 30 ga watan Ramadan.
Musulmi a waɗannan ƙasashe za su yi dakon sanarwa daga shugabanninsu domin tabbatar da ranar hawan idin karamar sallah watau Eid-ul-Fitr.
Ranakun hutun sallah a wasu ƙasashe
Gwamnatoci a duniya sun ayyana ranakun hutu na musamman don bai wa mutane damar yin shagalin sallah tare da iyalansu.
Saudiyya ta ayyana hutun kwanaki huɗu daga 30 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, tare da komawa bakin aiki a ranar 3 ga Afrilu.
Idan aka haɗa da hutun Juma'a da Asabar, ma’aikata masu zaman kansu na iya samun hutu na kwanaki shida.

Asali: Getty Images
UAE ta tabbatar da hutun kwanaki uku daga 1 zuwa 3 ga Shawwal, tare da yiwuwar karin yini guda idan Ramadan ya cika kwanaki 30.
Kuwait ta bayar da hutun kwanaki uku idan sallah ta faɗo a 30 ga Maris, amma idan ta zo a 31 ga Maris, ma’aikata za su sami hutu mai tsawo na kwanaki tara.

Kara karanta wannan
"Ba ni da hannu," Sheikh Sulaimon ya fashe da kuka a tafsirin Ramadan, ya rantse da Alƙur'ani
Qatar da Bahrain su ma sun sanar da ranakun hutu masu tsawo daga kwanaki uku zuwa shida.
Sultan ya ja hankalin al'ummar musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa mai alfarma sarkin Musulmi ya yi wa jama'a nasiha yayin da azumin Ramadan ya fara bankwana.
Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya roki al'ummar musulmi su ci gaba da aikata ayyukan alheri kuma su kaucewa saɓon Allah ko bayan fitar watan Ramadan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng