Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa kan Ganin Watan Ramadan na 2025

Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa kan Ganin Watan Ramadan na 2025

  • Rahotanni na nuni da cewa kotun kolin Saudiyya ta bukaci a fara duban watan Ramadan a yammacin Jumu’a, 29 ga Sha’aban 1446
  • Hukumar hasashen yanayi ta bayyana cewa za a samu hadari a wasu yankunan yayin da sararin samaniya na nan garau a wurare
  • Hukumomi sun ce za a sanar da sakamakon binciken duba jinjirin Ramadan da misalin karfe 6:00 na yamma a agogon Makkah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Gwamnatin Saudiyya ta bukaci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Ramadan a yammacin yau Jumu’a, 29 ga Sha’aban 1446, domin tantance ranar farko ta azumin bana.

Kotun koli ta Saudiyya ce ta fitar da wannan sanarwa, inda ta bukaci duk wanda ya hango jinjirin wata, ko dai da ido ko ta amfani da na’ura, da ya kai rahoto ga kotu mafi kusa.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Ramadan
Ana shirye shiryen duba watan Ramadan a Saudiyya. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Kasar Saudiyya ta bayyana haka ne a cikin wani sako da shafin yanar gizon kasar na Inside the Haramain ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro cewa za a sanar da sakamakon binciken jinjirin wata da misalin karfe 6:00 na yamma a agogon Makkah.

Yanayin sararin samaniya yayin duban wata

A cewar hukumar hasashen yanayi, za a sami hadari a wasu yankunan Saudiyya yayin duban jinjirin watan Ramadan.

Jihohin da ake sa ran samun hadari ko gajimare sun hada da Riyadh, Makkah, Madinah, Al-Qassim da yankin gabashin Saudiyya.

Sai dai a yankunan iyakar arewa, Al-Jawf, Hail, Tabuk, Najran da Jazan, ana sa ran sararin samaniya zai kasance garau, wanda hakan zai ba da damar ganin jinjirin wata cikin sauki.

Saudiyya ta bukaci mutane su bayar da rahoto

Kotun kolin Saudiyya ta bukaci Musulmi su yi kokarin duban jinjirin watan Ramadan a yau da yamma, domin tabbatar da ranar farko ta azumin bana.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Masana taurari sun fadi ranar ganin watan Ramadan a Najeriya

An bukaci duk wanda ya hango watan, ta ido ko da amfani da na’ura, da ya sanar da kotu mafi kusa domin tabbatar da sahihancin rahoton.

Binciken ganin watan zai gudana a fadin Saudiyya, inda ake sa ran sanar da sakamakon binciken da misalin karfe 6:00 na yamma agogon Makkah.

Yawata
Yadda ake shirye shiryen duba wata a Saudiyya. Hoto: Inside The Haramain
Asali: Twitter

Ana sa ran sanar da sakamakon bincike

A yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon binciken jinjirin watan Ramadan, gwamnati da hukumomi sun tabbatar da shirin gudanar da azumi cikin nasara.

Sanarwar da za a fitar daga Saudiyya a yammacin yau za ta tantance ranar farko ta azumin bana ga Musulmi a fadin kasar.

Musulmi a kasashen duniya na ci gaba da sa ido kan wannan bincike, wanda zai kasance daya daga cikin manyan al’amuran da ke kayatar da al’umma a duk shekara.

Za a fara duba watan Ramadan a Najeriya

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fitar da sanarwa ga musulmi kwanaki 2 kafin fara azumin Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa fadar mai alfarma sarkin Musulmi ta bukaci a fara duba jinjirin wata a fadin Najeriya a yammacin ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu.

An fitar da sanarwar cewa duk wanda ya kalli watan ya garzaya masarauta mafi kusa ko kuma ya tuntubi wasu lambobin waya da aka bayar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng