Komai na Iya Faruwa: Fafaroma Francis Yana cikin Mummunan Halin Rashin Lafiya
- Fadar Vatican ta tabbatar cewa Fafaroma Francis yana cikin mawuyacin hali bayan matsalar numfashi
- Bisa ga bayanin likitoci, Fafaroma yana fama da rashin jini da kuma 'thrombocytopenia' inda yake cikin hayyacinsa
- Magoya bayan Fafaroma sun taru a asibitin Gemelli suna addu’a, inda Vatican ta ce ba zai yi hudubar Angelus ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Roma, Italy - Fadar Vatican ta tabbatar cewa Fafaroma Francis, mai shekaru 88, yana cikin mawuyacin hali bayan matsalar numfashi.
Fadar ta tabbatar da haka ne a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairun 2025 inda ta sa aka ba shi iskar 'oxygen' mai ƙarfi da jini.

Asali: Getty Images
Fafaroma Francis yana fama da jinya mai tsanani
Fox News ta ce Pope na shirin kwana na tara a asibitin Gemelli da ke Rome bayan gano yana da ciwon huhu mai tsanani.

Kara karanta wannan
Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"Halin Fafaroma Francis yana da matukar hatsari; don haka, kamar yadda aka faɗa jiya, har yanzu bai fita daga haɗari ba.
"Da safe, Pope Francis ya fuskanci matsananciyar matsalar numfashi ta 'asthma' wanda ya sa dole a ba shi iskar oxygen mai ƙarfi."
Gwaje-gwajen jini sun nuna yana fama da 'thrombocytopenia' da rashin jini, lamarin da ya sa likitoci suka ba shi jini don inganta lafiyarsa.
Duk da wannan yanayi, Vatican ta ce Fafaroma yana cikin hayyacinsa kuma ya kwana yana zaune a kujera, kodayake yana jin wahala fiye da yadda yake ji jiya.
Vatican ta tabbatar cewa Fafaroma Francis ba zai gudanar da addu’ar Angelus da aka saba yi kowanne Lahadi ba, za a wallafa rubutaccen saƙonsa kamar yadda aka yi makon da ya gabata.

Asali: Facebook
Faman da Fafaroma Francis ya sha a jinya
Fafaroma Francis ya jagoranci cocin Katolika tun daga 2013 amma ya fuskanci matsalolin lafiya da dama, ciki har da tiyata a 2021 da 2023, cewar rahoton BBC.
Sakataren Harkokin Wajen Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya ce irin waɗannan tattaunawa suna yiwuwa amma bai so ya shiga “shawarwarin da ba su da amfani” ba.
Ya ce:
“A yanzu, damuwarmu ita ce lafiyar Fafaroma, murmurewarsa da dawowarsa Vatican, wadannan ne muhimman abubuwa."
A wajen asibitin Gemelli, ‘yan uwa sun taru suna addu’a don samun sauƙin Pope Francis.
Vatican ta ce Fafaroma yana sauyawa tsakanin gado, kujera, da kuma ɗakin ibada na musamman a cikin ɗakinsa, inda yake addu’a kuma yana ci gaba da aikinsa.
Shugaban ƙungiyar likitocin Fafaroma a Gemelli, Farfesa Sergio Alfieri, ya ce a ranar Juma’a an samu ƙaramin ci gaba, wanda ya sa likitoci suka rage magungunansa.
Ya ce:
“Shin Fafaroma ya fita daga haɗari? A’a, bai fita daga haɗari ba, amma idan kana tambaya ko yana cikin haɗarin mutuwa a yanzu, amsar ita ce a’a.”
Fafaroma Francis ya fadi kalubalen rasuwarsa
Kun ji cewa Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis ya bayyana yadda ya rika tsallake harin 'yan kunar bakin wake a Iraqi.
Fafaroman ya bayyana cewa sai da aka ja kunnensa da cewa kar ya ziyarci kasar, duba da kalubalen da ke tattare da hakan.
Asali: Legit.ng