Trump: Sojojin Amurka za Su Fara kai Zafafan Hare Hare kan Boko Haram

Trump: Sojojin Amurka za Su Fara kai Zafafan Hare Hare kan Boko Haram

  • Shugaban sojojin saman Amurka a Turai da Afirka, Janar James Hecker, ya ce za su kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a nahiyar Afirka
  • Janar Hecker ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da kai farmaki kan kungiyoyin da ke barazana ga kasashen Afirka da Amurka
  • A yayin taron hafsoshin sojin sama na Afirka, an tattauna batun hadin gwiwa kan tsaro da tallafin jin kai da yadda za a kakkabe 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sojojin saman Amurka sun bayyana shirin su na kai farmaki kan kungiyoyin ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na nahiyar Afirka.

Shugaban rundunar sojin saman Amurka a Turai da Afirka, Janar James Hecker, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da aka yi da shi yayin taron hafsoshin sojin saman Afirka.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

Jirgin yaki
Amurka za ta farmaki 'yan ta'ada a Afrika. Hoto: Nigeria Air Force HQ
Asali: Getty Images

Gwamnatin Amurka ta wallafa a shafinta cewa an shirya wannan taron ne domin tattauna batun hadin gwiwar tsaro da kuma yadda za a tallafawa kasashen Afirka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka za ta farmaki 'yan ta'addan Afrika

Janar James Hecker ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke barazana ga kasashen Afirka da Amurka.

“Kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar ISIS na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar kasashen Afirka da Amurka.
"Don haka za mu ci gaba da kai hare-hare kan wadannan kungiyoyi a nahiyar.”

- Janar James Hecker

Haka zalika, ya bayyana cewa Amurka ta riga ta kai farmaki kan ISIS a Somaliya, kuma irin wannan matakin ne za a dauka a wasu sassan Afirka domin tabbatar da tsaro.

A karkashin haka ne ake ganin Amurka za ta kai zafafan hare hare kan 'yan Boko Haram da wasu 'yan ta'addan Afrika.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

Amurka za ta tallafawa Najeriya

Da yake magana kan yaki da Boko Haram a Najeriya, Janar Hecker ya bayyana cewa Amurka na ci gaba da bai wa Najeriya horo da kayan aiki domin yakar ta’addanci.

Vanguard ta rahoto cewa Janar James Hecker ya ce:

“Tun tuni gwamnatin Amurka ke bai wa Najeriya horo da kayan aiki, kuma muna fatan hakan zai taimaka wa kasar wajen yaki da ‘yan ta’adda.”

Sai dai ya bayyana cewa taron da aka gudanar bai mayar da hankali kan samun rinjaye a yakin sama ba, illa dai yadda kasashen Afirka za su iya taimaka wa junansu ta hanyoyi daban-daban.

Tinubu
Shugaba Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|Donald J. Trump
Asali: Facebook

Kasashen Afirka za su hada kai

Shugaban rundunar sojin saman Zambiya, Laftanal Janar Oscar Nyoni ya ce kasashen da ke cikin hadin gwiwar AACS za su hada kai domin tallafawa wadanda bala’i ya shafa.

Laftanal Janar Oscar Nyoni ya ce:

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Trump zai binciki zargin tallafawa Boko Haram daga Amurka

“Ta hanyar wannan hadin gwiwa, idan wani bala’i ya faru, za a iya samar da abinci, kayan agaji da kuma kayan aiki daga kasashen da ke cikin wannan kungiya.”

Laftanal Janar Nyoni ya kara da cewa hadin gwiwar da ake da shi tsakanin kasashen Afirka da Amurka zai taimaka matuka wajen saukaka jigilar kayan agaji da kuma samar da tallafi.

Amurka za ta binciki tallafawa Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka za ta yi bincike kan zargin cewa ana amfani da kudin USAID wajen tallafawa Boko Haram.

Gwamnatin Donald Trump za ta kafa kwamitin binciken ne yayin da wani dan majalisar Amurka ya yi zargin a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng