An Samu Masu Nuna Rashin Ladabi a Kabarin Annabi SAW, Sudais Ya Yi Gargadi
- Sheikh Dr Abdur Rahman As-Sudais ya yi gargadi kan daga murya a kabarin Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa hakan bai dace ba
- Babban limamin ya yi kira ga a'lummar Musulmi da suka samu damar kai ziyara masallacin Annabi SAW da ke Madina da su rika girmama shi
- Malamai sun yi nuni da cewa dole ne Musulmi su daraja Annabi (SAW) fiye da kowa domin masa biyayya ita ce biyayya ga Allah SWT mai girma
- Wani malamin addini a Najeriya ya bukaci hukumar alhazai ta Najeriya da ta rika daukar matakin wayar da kan maniyyata kan lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Shugaban kula da harkokin addini na Masallacin Harami, Sheikh Dr Abdur Rahman As-Sudais, ya jaddada muhimmancin girmama kabarin Annabi Muhammad (SAW).
Malamin ya yi magana yana mai gargadin Musulmi da su guji daga murya ko nuna rashin ladabi a wajen kabarin.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a cikin wani sako da shafin kasar Saudiyya na Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Saleh Al-Munajjid ya bayyana cewa dole ne Musulmi su daraja Annabi (SAW) fiye da komai a rayuwarsu.
Gargadin Sudais kan daraja Annabi Muhammad (SAW)
Sheikh Dr. Abdur Rahman As-Sudais ya yi kira ga dukkan musulmi da su mutunta kabarin Annabi (SAW) ta hanyar yin shiru da kuma nuna ladabi a wannan muhalli mai alfarma.
Ya nakalto ayar Al-Kur’ani mai girma da ke cewa wadanda suke kasa-kasa da muryoyinsu a gaban Manzon Allah (SAW) su ne masu imani kuma suna da lada mai yawa.
Malamin ya ce wajibi ne a girmama Annabi SAW yana raye da bayan rasuwarsa, saboda daga murya a kabarinsa kamar daga murya ne a lokacin da yake da rai a gabansa.
Sheikh Sudais ya yi kira ga masu ziyartar Masallacin Annabi (SAW) da su ribaci damar samun lada mai yawa ta yin salloli a cikinsa.
Maganar kauna da daraja Annabi (SAW)
Sheikh Saleh Al-Munajjid ya wallafa dalilan da ya sa dole ne musulmi su nuna kauna ga Manzon Allah (SAW) fiye da komai a shafinsa da ya ke amsa tambayoyi.
Malamin ya ce Allah ya umarci Musulmi da biyayya ga Manzon Allah (SAW) a cikin Al-Kur'ani mai girma.
Sheikh Saleh Al-Munajjid ya bayyana cewa biyayya ga Manzon Allah (SAW) biyayya ce ga Allah kamar yadda Al-Kur'ani ya tabbatar.
A karkashin haka, Sheikh Al-Munajjid ya ce duk wanda ya ki bin koyarwar Annabi (SAW), to ya sabawa Allah.
Hadarin rashin daraja Annabi SAW
Sheikh Saleh Al-Munajjid ya ce Allah ya yi gargadi ga wadanda ba sa daraja Manzonsa da cewa fitina za ta iya samunsu.
A karkashin haka aka gargadi masu kai ziyara Madina da su rika kaucewa daga murya a kabarin Manzon Allah domin kar su shiga cikin gargadin da Allah ya yi.
Legit ta tattauna da malamin addini
Wani malamin addini, Ustaz Muhammad Abubakar ya bukaci hukumar alhazai da ta rika wayar da kan maniyyata.
Malamin ya ce:
"Hakan ya saba shari'a, amma hanyar da za a kaucewa laifin cikin sauki ita ce wayar da kan maniyyata kafin tafiya kasa mai tsarki."
An yi nasiha ga malaman kungiyar Izala
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yi nasiha ga malaman kungiyar Izala da ke sukar juna.
Sheikh Asadussunnah ya ce akwai bukatar Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Sani Yahaya Jingir da su daidaita tsakaninsu, su daina rigima da juna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng