An Shiga Jimami bayan Jirgin Sama Dauke da Mutane Ya Rufto daga Sararin Samaniya

An Shiga Jimami bayan Jirgin Sama Dauke da Mutane Ya Rufto daga Sararin Samaniya

  • An ƙara shiga jimami a ƙasar Amurka bayan sake samun iftila'in hatsarin jirgin sama a ranar Juma'a, 31 ga watan Janairun 2024
  • Hatsarin jirgin saman dai ya auku ne a yankin Arewa maso Gabashin birnin Philadelphia na jihar Pennsylvania a karshen makon nan
  • Rahotanni sun nuna akwai mutane shida a cikin jirgin wanda yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Springfield-Branson a Missouri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Amurka - An samu aukuwar hatsarin wani ƙaramin jirgin sama na musamman a Arewa maso Gabashin birnin Philadelphia ta ƙasar Amurka a ranar Juma'a.

Kafofin watsa labarai suna nuna hoton wutar gobara da ta tashi a ƙasa cikin unguwar da jirgin ya faɗo wacce ta cika da gidaje da kasuwanni.

Jirgin sama ya yi hatsari a Amurka
Jirgin sama ya rufto daga sararin samaniya a Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mutane nawa ne a cikin jirgin saman?

Hukumar jiragen sama ta tarayya (FAA) ta tabbatar da cewa akwai mutane shida a cikin jirgin na Learjet, amma ba a samu tabbacin ko akwai wanda ya tsira ba, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Max Air ya fitar da bayanai a kan hatsarin jirginsa a Kano, an rufe titin saukar jirage

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin ya fadi da misalin karfe 11:30 na dare a cikin wani yanki mai yawan jama'a a cikin birnin, wanda ke ɗauke da gidaje, shaguna, da hanyoyin mota masu cunkoson ababen hawa.

Hukumar FAA ta bayyana cewa jirgin yana kan hanyar zuwa filin jirgin saman Springfield-Branson na birnin Missouri, bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Arewa maso Gabashin Philadelphia,

FAA ta tabbatar da cewa za ta gudanar da bincike tare da hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar.

Sakataren ma'aikatar sufurin Amurka, Sean Duffy, ya ce akwai "rahoton cewa" akwai mutane shida a cikin jirgin.

Babu wani tabbaci game da samun asarar rayuka sakamakon hatsarin jirgin.

Wane ƙoƙari hukumomi suke yi kan hatsarin?

Gwamnan jihar Pennsylvania ya bayyana cewa sun ba da kayan ga masu ba da agajin gaggawa domin ceto mutanen da lamarin ya ritsa da su.

Faɗuwar jirgin a birnin na gabashin Amurka ta zo ne kwanaki biyu bayan hatsarin wani jirgin fasinjoji da jirgi mai saukar ungulu na sojoji a kusa da filin jirgin sama na Reagan a birnin Washington.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Hatsarin ya jawo asarar rayukan kusan mutane 67, lamarin da ya zama mafi munin hatsarin jirgin sama a Amurka a cikin kusan shekara 50.

Jirgin na Learjet da ya fadi na daya daga cikin jiragen da ake amfani da su wajen daukar marasa lafiya, kamar yadda shafin lura da tashi da saukar jiragen sama, FlightAware, ya bayyana.

Jirgin sama na Max Air ya yi hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa jirgin sama na kamfanin Max Air ɗauke da fasinjoji ya gamu da hatsari a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Jirgin saman ɗauke da fasinjoji daga jihar Legas ya gamu da hatsarin ne a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Jirgin saman wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma'aikata shida ya rasa taƴar gabansa ne bayan ya sauka a filin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel