Trump Ya Fara Farautar Baki, Za a Koro 'Yan Najeriya Mutane 5,144 Gida
- Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin Amurka karkashin shugaba Donald Trump na shirin korar ’yan Najeriya 5,144 daga kasar
- Ana zargin cewa daga cikin wadanda abin ya shafa na da laifuffuka, wasu kuma sun karya dokokin shige da fice yayin zamansu a Amurka
- A kokarin yayyafa ruwa ga wutar, gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti domin shawo kan lamarin musamman idan aka koro su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Gwamnatin Amurka na shirin korar ’yan Najeriya 5,144 daga kasar a matakin farko na sabon tsarin shige da fice da shugaba Donald Trump ya aiwatar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sabuwar dokar da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa domin kawar da bakin haure marasa takardu daga kasar.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa wadanda lamarin ya shafa sun hada da ’yan Najeriya da ke karkashin hukumar shige da fice ta Amurka (ICE) da sauran wadanda aka yanke wa hukuncin kora.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Najeriya da za a kora a kasar Amurka
Rahotanni daga ICE sun nuna cewa a yanzu akwai jimillar mutane 1,445,549 daga kasashe daban-daban da ke fuskantar korar gaggawa daga Amurka, inda daga cikinsu 3,690 ’yan Najeriya ne.
Haka kuma, an tabbatar da cewa akwai karin ’yan Najeriya 1,454 da ke tsare a hannun ICE, wadanda za a mayar da su Najeriya nan ba da dadewa ba.
Daga cikin wannan adadi, 772 na tsare ne bisa dalilai na aikata laifuffuka ko tuhuma, yayin da sauran suka karya dokokin shige da fice.
Rahoton ya kara da cewa daga shekarar 2019 zuwa watan Nuwamba na shekarar 2024, an riga an mayar da ’yan Najeriya 884 daga Amurka, kuma 417 aka kora a shekarar 2024 kadai.
Sabuwar dokar shige da ficen Trump
Punch ta wallafa cewa sabuwar dokar da Shugaba Donald Trump ke aiwatarwa ta mayar da hankali kan kawar da bakin haure marasa takardu daga kasar.
A cikin kwanaki kadan da fara aikin wannan doka, an riga an kama kimanin mutane 3,000 da ake zargin sun aikata laifuffuka.
Ko da yake a farko an fi mayar da hankali kan wadanda ke da laifuffuka, akwai fargabar cewa gwamnatin Amurka za ta fara kama sauran bakin hauren da ba su da takardun izinin zama.
Masu fuskantar wannan matsala su ne wadanda suke cikin jerin sunayen mutanen da ICE ke shirin kora daga Amurka duk da cewa ba a tsare suke ba.
Matakin gwamnatin Najeriya kan kora a Amurka
A halin yanzu, kokarin jin ta bakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya kan lamarin bai yi nasara ba.
Sai dai Hukumar ’Yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman domin shawo kan matsalar idan har aka fara korar.
Jami’in hulda da jama’a na NiDCOM, Abdurahman Balogun, ya ce:
"Gwamnati ta kafa kwamiti na musamman wanda ya hada da Ma’aikatar Harkokin Waje, NiDCOM,
"Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da kuma Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, domin shawo kan matsalar idan har Amurka ta fara kora ’yan Najeriya."
Trump ya dakatar da tallafawa Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta dakatar da tallafawa Najeriya da wasu kasashen duniya.
Donald Trump ya ce Amurka ba za ta cigaba da sanya kudinta a wasu kasashe ba matukar ba amfani Amurkawa za su samu daga tallafin ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


