Abubuwa 10 Game da Ɗan Shugaban Amurka Trump da Ya Karfafa Nasararsa a Zaben 2024

Abubuwa 10 Game da Ɗan Shugaban Amurka Trump da Ya Karfafa Nasararsa a Zaben 2024

  • Donald Trump, dan shekaru 78, ya zama shugaban Amurka na 47, kuma wannan ne karo na biyu da zai jagoranci babbar kasar
  • Iyalan Trump, ciki har da Melania da ɗansa Barron mai shekara 18, sun halarci rantsarwar da aka yi a Capitol da ke Washington, DC
  • Legit Hausa ta jero wasu muhimman abubuwa 10 game da Barron, wanda Trump ya ce ya taimaka masa wajen lashe zaben 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Fitaccen dan kasuwa, Donald Trump, ya zama shugaban Amurka na 47, a ranar Litinin, kuma wannan ne karo na biyu da zai jagoranci kasar.

An rantsar da Trump mai shekaru 78 a dakin taro na West Front da ke cikin babban ginin majalisar kasar, watau Capitol da ke Washington, DC.

Trump ya yi magana a kan dansa Barron da aka rantsar da shi matsayin shugaban Amurka na 47
Trump ya jinjinwa dansa Barron a matsayin wanda ya karfafi matasa suka zabe shi a 2024. Hoto: Pool, Joe Raedle
Asali: Getty Images

Iyalan Donald Trump sun halarci rantsar da shi

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

Iyalin Trump, ciki har da matar sa, Melania, da ɗansa mai shekaru 18, Barron Trump, duk sun halarci bikin, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin rantsar da shugaban ya ja hankalin jama’a musamman bayan Trump ya gabatar da ɗansa mai tsayin kafa bakwai ga taron jama’ar da suka zo taya shi murna.

Trump ya danganta nasarar lashe zaɓensa ga ɗansa, wanda ya shawo kan matasa sa’anninsa suka zaɓe shi ta hanyar gabatar da shirye-shiryen podcasts.

Abin da Trump ya ce game da ɗansa

A wajen taron, Donald Trump ya ce:

“Ina da ɗa mai tsawo sosai mai suna Barron. Shin akwai wanda ya taɓa jin labarinsa? Shi ya lakanci sirrin jawo ra'ayin matasa su yi zaɓe.
"Kun san mun samu ƙuri’un matasa da tazarar maki 36 kuma shi ne ya rika cewa, ‘Baba, dole ne ka fita ka yi wannan da wancan.’ Mun yi su da yawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

“Kuma yana girmama duk wanda ya hadu da shi; ya fahimce su sosai. Ya kan ce, ‘Dole ne ka fita. Ka yi hira da Joe Rogan, ka yi hira da waɗannan mutanen, kuma mun yi su duka.”

Muhimman abubuwa 10 game da Barron Trump

A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta bankado bayani game da ɗan gadon mulkin Trump.

1. Haihuwa

An haifi Barron Trump a ranar 20 ga watan Maris din shekarar 2006, a matsayin ɗa ɗaya dilo ga Donald da Melania Trump, inji rahoton USA Today.

2. Shahara a fuskar jama’a

An sha jin labaran Barron tun lokacin da mahaifinsa ya hau mulki a shekarar 2016, musamman saboda tsawonsa na ban mamaki wanda ya kai kafa 6 da inci 9.

3. Ilimi

A ranar 17 ga Mayu, 2024, Barron ya kammala karatunsa daga Oxbridge Academy da ke West Palm Beach, Florida, kuma yanzu ɗalibi ne a jami’ar New York.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

4. Mu'amalarsa da mutane

An san Barron da saukin kai, kuma ba ya yawan murmushi a bainar jama’a.

5. Kwarewar harsuna

Baron ya na magana da harsuna da dama, ciki har da Faransanci, Sifaniyanci, Turanci, da Ingilishin Slovenian na mahaifiyarsa.

6. Tsare-rsaren rayuwa

Punch ta rahoto cewa mahaifiyarsa, Melania Trump ce ke kula da abincin Barron da abubuwan da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum.

7. Tasirinsa a siyasa

Donald Trump ya taɓa kiran Barron a matsayin wani sashe na "sabon ƙarni na manyan masu ba shi shawara" bayan ɗan saurayin ya bayar da shawarwari kan yakin neman zaɓensa a 2024.

8. Zaɓen farko

Barron ya fara kada ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa na 2024.

9. Matsayi a iyali

A matsayinsa na ƙaramin ɗa a cikin ’ya’yan Donald Trump, ana hasashen cewa Barron ne zaai gaji daular shugaban kasar na Amurka.

10. Wasanni

An ce Barron yana sha'awar wasanni sosai, inda ya taka leda a lokacin da yake makarantar gaba da sakandare.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Donald Trump ya cire Amurka daga WHO

A wani labarin, mun ruwaito cewa Donald Trump ya sanar da ficewar Amurka daga WHO, yana zargin ta da gazawa wajen magance COVID-19.

WHO ta nuna damuwa kan matakin Amurka, kasancewarta babbar mai ba da gudummawa, tana mai cewa wannan barazana ce ga yaki da tarin fuka da HIV/AIDS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.