Sabuwar Matsala: Amurka Ta Yi Abin da Ya Jawo Man Fetur Ya Ƙara Kuɗi a Duniya
- Farashin danyen mai ya kara kudi zuwa $81, mafi tsadarsa cikin watanni hudu, sakamakon takunkumin Amurka kan Rasha
- Takunkumin ya tilasta wa kasashen China da India sayen mai daga Gabas ta Tsakiya, Afrika, wanda ya jawo tsadar mai
- Rahotanni sun nuna cewa manyan rumbunan ajiya sun ƙara farashin fetur daga N908 zuwa tsakanin N950 zuwa N960 a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Farashin danyen man Brent ya kara kudi zuwa $81 a kan kowace ganga, wanda ya kai kololuwar tsadarsa a cikin watanni hudu.
Man Brent ya tashi da $1.40 (kimanin karin kaso 1.8%), yayin da man WTI ya tashi da $2.15 (kimanin karin kaso 2.8%).
Wannan karin farashin Brent na nuna mafi tsadarsa tun ranar 26 ga watan Agusta, yayin da WTI ya kai kololuwar tsadarsa tun 12 ga Agusta, 2024, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene ya haifar da tashin farashin danyen mai?
Karin farashin na da alaka da sababbin takunkumi da Amurka ta kakaba wa masana'antar man fetur ta Rasha a makon da ya gabata.
Ma’aikatar baitulmali ta Amurka ta haramta wa wasu kamfanonin Rasha sufurin mai, ciki har da Gazprom Neft da Surgutneftegaz.
An kuma hada da haramcin tafiye-tafiyen wasu jiragen ruwa 183 da suke jigilar danyen mai daga Rasha zuwa kasashe daban-daban.
Dalilin Amurka na kakabawa Rasha takunkumi
Amurka na ganin takunkumin zai rage kudaden shiga da Rasha ke samu daga danyen mai wanda ake amfani da shi wajen daukar nauyin yakin da take yi da Ukraine.
Masana tattalin arziki sun ce wannan takunkumi zai tilasta wa kasashe kamar China da India sayen mai daga Gabas ta Tsakiya, Afrika da kuma Amurka.
Hakan zai sa farashin kasuwanci da kudin sufuri su karu, wanda zai kara tasirin farashin mai a kasuwannin duniya.
Duk da haka, akwai fargaba kan yadda farashin zai kasance idan Donald Trump ya karbi mulki a matsayin shugaban Amurka a mako mai zuwa.
Matsalar da takunkumin za ta haifarwa kasuwar mai
Bayan sanar da takunkumin, jiragen ruwa 65 dauke da danyen mai sun tsaya a bakin teku a kasashe kamar China da Rasha.
A makonni uku da suka gabata, farashin mai ya tashi sosai saboda raguwar adadin mai a gidajen ajiya na Amurka.
Gwamnatin Joe Biden ta kakaba takunkumi kan masana'antun man fetur na Rasha, jiragen ruwa, da dillalai, da nufin dakile duk wata hanyar sayar da mai.
Wannan takunkumi na iya haddasa karancin mai a kasuwannin duniya, duk da cewa karfin dala na iya takaita tashin farashin man.
Wane mataki 'yan kasuwar mai suka dauka?
Taron gaggawa ya gudana tsakanin ‘yan kasuwa a China da India, inda suke nazarin yadda takunkumin zai shafi shigo da danyen mai.
Rahoton Business Standard ya nuna cewa kamfanonin kasar China suna binciken yiwuwar karbar danyen mai da ke kan hanya kafin takunkumin ya fara aiki.
A India kuwa, an fara fargabar yuwuwar cikas ga shigo da mai a watanni masu zuwa, wanda zai iya tsawaita wannan tasiri.
Masana suna bibiyar tasirin wannan takunkumi a kasuwannin makamashi na duniya, suna kuma fargabar ci gaba da samun karancin mai.
Farashin dakon mai ya karu a Najeriya
A wani labarin, mun rahoto cewa takunkumin da Amurka ta kakabawa Rasha ya fara tasiri a kasuwannin mai, inda aka kara kudin dakon mai a Najeriya.
Sakamakon tsadar mai a duniya, 'yan kasuwar man Najeriya sun ƙara farashin fetur da dizil a manyan rumbunan ajiya da N43, wanda ya kai ƙarin kaso 4.74%.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng