An Shiga Jimami bayan Dan Majalisa Ya Bindige Kansa, an Gano Dalili

An Shiga Jimami bayan Dan Majalisa Ya Bindige Kansa, an Gano Dalili

  • Tsautsayi ya ritsa da wani ɗan majalisar dokoki a ƙasar India, bayan ya harbe kansa har lahira bisa kuskure
  • Gurpreet Gopi na jam'iyyar AAP ya yi harbi bisa kuskure wanda hakan ya jawo ya samu mummunan rauni a kansa
  • Jami'an rundunar ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ƙara da cewa za a gano ainihin musabbabin mutuwarsa bayan an yi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kasar India - Wani ɗan majalisar dokokin India, Gurpreet Gogi, ya harbe kansa bisa kuskure wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa.

A cewar ƴan uwansa, ɗan majalisar na jam’iyyar Aam Admi Party (AAP) ya harbi kansa bisa kuskure, wanda hakan ya jawo samun mummunan rauni a kansa.

Dan majalisa ya rasu a India
Gurpreet Gopi ya rasu sakamakon harbin bindiga Hoto: @DainikShaamTak @IshaniKrishnaa
Asali: Twitter

Ɗan majalisa ya mutu a India

Jaridar Gulf News ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da tsakar dare, inda aka garzaya da shi zuwa Asibitin Dayanand Medical College (DMC), amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta yi bayani a kan sace sama da N1bn daga asusun gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa Gurpreet Gogi an same shi ne a mace a daren Juma’a tare da raunin harbin bindiga a jikinsa.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Wani jami’in ƴan sandan Punjab ya tabbatar da mutuwar, inda ya ce alamu sun nuna cewa lamarin kamar ba da gangan ya faru ba, rahoton socialnews ya tabbatar.

Da yake magana da manema labarai, mataimakin kwamishinan ƴan sanda (DCP) Jaskaran Singh Teja ya tabbatar da aukuwar lamarin.

DCP ɗin ya ƙara da cewa ainihin dalilin mutuwar ɗan majalisar zai bayyana ne bayan rahoton binciken gawa ya fito.

"A cewar ƴan uwansa, ya harbi kansa bisa kuskure, wanda hakan ya jawo ya samu raunin harbin bindiga a kansa."
"An tabbatar da mutuwar Gurpreet Gogi a asibiti, kuma an ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawa na asibitin DMC.”
"Dalilin mutuwar zai bayyana ne da zarar an kammala rahoton binciken gawar."

Kara karanta wannan

Yadda zargin Peter Obi ya jefa rayuwarmu a cikin barazana," Kakakin APC

- Jaskaran Singh Teja

An fara gudanar da bincike

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano cikakkun bayanai dangane da lamarin.

Gurpreet Gogi, wanda ya shiga jam’iyyar AAP a shekarar 2022, ya ja hankalin jama’a bayan ya kayar da Bharat Bhushan Ashu, a lokacin zaɓen majalisar dokoki na Ludhiana.

A wani lamari makamancin haka, a shekarar 2019, wani ɗan takarar majalisar dokokin jihar Mississippi, Carl Robinson, ya harbe matarsa, Latoya Thompson, har lahira sannan ya kashe kansa bayan ta nemi ya saketa.

Wannan lamari ya sake jaddada muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da magance damuwa, musamman ga shugabanni masu matsayi, domin gujewa abubuwan da za su iya janyo hatsari ko tashin hankali.

Haka kuma, yana ƙarfafa gwiwar hukumomi su binciko cikakken dalilin mutuwar Gurpreet Gogi domin kawar da shakku a zukatan al’umma.

Mutane sun mutu a India

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutane a India bayan sun yi tatul da giya a yankin Tamil Nadu.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda jami'in tsaro ya rasa ransa bayan ceto mutanen da aka sace

Hukumomi a ƙasar India.sun tabbatar da cewa mutane aƙalla suka yi asarar rayukansu a lamarin wanda ya auku a Kallakurichi na yankin Tamil Nadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng