Yan Ta'adda Sun Kai Hari Fadar Shugaban Ƙasa, Dakarun Sojojin Chadi Sun Dura Kansu

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Fadar Shugaban Ƙasa, Dakarun Sojojin Chadi Sun Dura Kansu

  • Wasu gungun ƴan ta'adda sun yi yunkurin kutsawa cikin fadar shugaban ƙasar Chadi a birnin N’Djamena amma ba su samu nasara ba
  • Dakarun rundunar sojojin ƙasar sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka yi masu luguden wuta kuma suka yi nasarar kashe wasu daga cikinsu
  • Mutane sun fara zaman ɗar-ɗar a babban birnin bayan jin karar harbe-harbe a kusa da fadar mulki amma gwamnati ta ce an shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Chadi - Rahotanni daga ƙasar Chadi sun nuna cewa wasu ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kusa da fadar shugaban ƙasa.

Sai dai dakarun sojin ƙasar Chadi sun yi nasarar murƙushe mayaƙan Boko Haram da suka kai hari a kusa da fadar shugaban ƙasar, tare da kashe da dama daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga, sun kubutar da mutanen da suka sace

Mahamat Deby.
Sojoji sun ragargaji mayakan Boko Haram da suka kai hari fadar shugaban kasa Hoto: DW
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta ce wannan harin ya faru ne a yammacin ranar Laraba, lamarin da ya jefa mazauna birnin N’Djamena cikin zaman ɗar-ɗar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'adda sun kai hari fadar shugaban ƙasa

Reuters ta ruwaito cewa ƴan ta'addan sun yi yunƙurin kutsawa cikin harabar fadar shugaban ƙasa a harin amma suka gamu da fushin sojoji.

A yayin haka, jerin gwanon motocin sojojin Chadi suƙa nufi wurin da harin ya faru cikin gaggawa domin magance lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan ƙungiyar ta'addancin sun gamu da ruwan wuta daga sojojin, wanda ya kai ga kashe wasu da kama waɗansu daga cikinsu.

Sojoji sun yi wa maharan luguden wuta

A wani bidiyo da aka wallafa a kafofin sada zumunta, an ga sojojin suna ruwan wuta kan ƴan ta'addan.

Sauran waɗanda sojojin suka kama kuma za su fuskanci hukunci bayan kammala bincike.

Tun farko dai da yammacin wannan rana, mazauna birnin N’Djamena suka fara jin ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar, abin da ya tada hankula.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban jam'iyya ya aike da sabon gargadi

Gwamnatin Chadi ta shawo kan lamarin

Sai dai daga baya, ministan kula da ababen more rayuwa na ƙasar, Aziz Mahamat Saleh, ya tabbatar wa al’umma cewa an shawo kan lamarin.

"Babu wani abin damuwa, an riga an magance matsalar," in ji shi.

Shi ma wani jami’in gwamnatin ƙasar Chadi, Abderaman Koulamallah, ya tabbatar da cewa an samu matsala kaɗan, amma komai ya dawo daidai.

Ya kuma wallafa wani bidiyo daga fadar shugaban ƙasar inda ya ce an murƙushe yunkurin tayar da zaune tsaye.

Wannan nasarar da dakarun Chadi suka samu tana nuna ƙarfin ikon ƙasar wajen yaki da ta’addanci, musamman a yankin da ya daɗe yana fama da hare-haren Boko Haram.

Faransa ta musanta ikirarin Jamhuriyar Nijar

A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Faransa ya musanta zargin da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi cewa ta haɗa kai da Najeriya da Benin da nufin tada mata hankali.

Kara karanta wannan

Tsohon jami'in gwamnatin El Rufai ya shiga matsala, bayan ICPC ta maka shi kotu

Faransa ta ce zargin ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe, inda ta tabbatar da cewa ba ta tattauna da kowane ƙasa da nufin jawo ma Jamhuriyar Nijar matsala ɓa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262