Faransa Ta Yi Magana kan Zargin Hada Kai da Najeriya ta Yamutsa Nijar

Faransa Ta Yi Magana kan Zargin Hada Kai da Najeriya ta Yamutsa Nijar

  • Faransa ta musanta zargin da shugabannin sojin Nijar suka yi cewa tana amfani da Najeriya da Benin domin tayar da yamutsi a kasar
  • Jakadan siyasa na ofishin jakadancin Faransa a Najeriya, Bertrand de Seissan, ya bayyana zargin a matsayin wanda babu gaskiya a cikinsa
  • Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya yi ikirarin cewa Faransa ta yi amfani da wasu kungiyoyin ta’addanci domin cimma wata manufa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kasar Faransa ta bayyana zargin da Nijar ta yi mata na cewa tana hada kai da Najeriya domin tayar mata da yamutsi a matsayin wanda ba shi da wani tushe ko makama.

Dama dai 'yan Najeriya da wasu kasashen duniya na jiran bayani daga kasar Faransa kasancewar bata ce komai tun da aka fara zancen.

Kara karanta wannan

'Magana ta fara fitowa': Hamza Al Mustapha ya fadi dalilin ganawa da El Rufa'i

Macron
Faransa ta musa zargin tayar da yamutsi a Nijar. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jakadan siyasa na ofishin jakadancin Faransa a Najeriya, Bertrand de Seissan ya musanta zargin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

De Seissan ya ce,

“Wannan zargi ba shi da tushe ko ma’ana. Babu wata tattaunawa ko shiri da aka taba yi tsakanin Faransa da Najeriya kan wannan batu.”

Zargin da Nijar ta yi wa kasar Faransa

Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya yi ikirarin cewa Faransa tana amfani da Najeriya da Benin a matsayin sansanin kulla makarkashiya domin tayar da hankula a Nijar.

A wata hira da ya yi cikin harshen Hausa, Tchiani ya zargi Faransa da tattaunawa da kungiyoyin ta’addanci a Najeriya, ciki har da Boko Haram, domin cimma burinta.

Shugaban Nijar
Shugaban sojin Nijar, , Abdourahamane Tchiani. Hoto: Kamal Abdullahi
Asali: Getty Images

Martanin Faransa kan zargin shugaban Nijar

Daily Trust ta wallafa cewa a martanin da ya yi, Bertrand de Seissan ya bayyana cewa Faransa ba ta taba yin wata tattaunawa da Najeriya ko wani shiri makamancin haka ba.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun saki bama bamai a Neja, an halaka 'yan ta'adda da dama

Bertrand de Seissan ya ce;

“Wannan zargi kawai yana nufin tayar da hankalin al’umma ne. Faransa ba za ta taba shiga wani irin shiri da zai haifar da rikici ko rashin zaman lafiya a yankin ba.”

Da dama daga cikin masana sun ce Najeriya da Faransa na da dangantaka mai karfi ta fannin tsaro da ci gaba amma hakan bai nufin za su hada baki su cuci Nijar.

Makomar dangantakar Faransa da Nijar

Zargin da Nijar ta yi na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin kasar da Faransa, musamman bayan kifar da gwamnatin dimokuradiyya a watan Yulin 2023.

Faransa, wacce ta kasance tsohuwar mai mulkin mallaka a Nijar, ta riga ta yi tir da juyin mulkin da aka yi, tare da goyon bayan kungiyar ECOWAS wajen dawo da tsarin dimokuradiyya a kasar.

A karkashin haka ake ganin alakar kasashen za ta kara dagulewa bayan zargin da shugaban sojin Nijar ya yi wa Faransa.

Kara karanta wannan

Karshen shekara: NDLEA ta tafka kwamushe a Legas da Kano, an kame fitaccen dan fim

Faransa ba za ta kafa sansani a Najeriya ba

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa ba ta da wani shiri na kafa sansanin sojin Faransa a Arewa.

Babban Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa labarin cewa Faransa za ta kafa sansani ba gaskiya ba ne kwata kwata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng