'Ƙarya Ta Ƙare': Wasu Ƴan Najeriya 2 Za Su Shafe Shekaru 40 a Gidan Yarin Amurka
- Wasu ‘yan Najeriya biyu za su yi zaman gidan yari a Amurka bisa damfarar wata mata dala 560,000 ta hanyar soyayyar ƙarya
- An ce mutanen biyu sun yi amfani da asusun bankin Amurka, Kanada da Malaysia don karɓar kuɗin daga wadda suka yaudara
- Kotu ta yanke masu hukunci bayan FBI ta gabatar da hujjojin sakonni da bayanan asusun bankunan da suka yi amfani da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Wasu 'yan Najeriya biyu; Olutayo Sunday Ogunlaja da Abel Adeyi Daramola na fuskantar daurin shekaru 40 a gidan yarin Amurka.
Wata kotun Amurka ce ta yanke musu hukuncin bayan samun su da laifin zambar soyayya, inda suka damfari wata mata $560,000.
Wannan bayanin ya fito ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar shari’ar Amurka ta fitar ranar Litinin, wacce jaridar Punch ta samu a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun Amurka ta daure 'yan Najeriya shekara 40
An samu nasarar yanke hukuncin ne bayan kwanaki hudu na shari’a da kuma awa uku kacal na tattaunawar alƙalai.
Ofishin lauyan gwamnatin Amurka ya bayyana cewa 'yan Najeriyar sun fara shirin damfarar a Janairun 2016 ta hanyar amfani da sunan ƙarya, “Glenn Brown."
Sun yi amfani da bayanan ƙarya a shafin yanar gizon soyayya na eHarmony.com, don kafa dangantaka ta soyayya da wata mata daga Albuquerque, New Mexico.
An bayyana cewa mutanen biyu 'yan asalin Najeriya da hadin bakin wasu sun karbi dubban daloli daga wadda suka yaudara.
Yadda 'yan Najeriya suka damfari 'yar Amurka
Sanarwar da Lauyan Amurka Alexander Uballez da Raul Bujanda na FBI suka sa hannu, ta yi karin bayani game da zambar mutanen.
"Sun yaudari matar ne don ta yi imani cewa tana taimaka wa “Glenn Brown” wajen kammala aikin gine-gine a Malaysia da shirin dawowarsa Amurka.
"Matar ta aika kimanin dala 560,000 zuwa wasu asusu daban-daban na Amurka, Kanada, da Malaysia tsakanin Janairun 2016 da Afrilun 2017.
"Ranar 27 ga Satumba, 2016, matar ta aika dala 28,000 zuwa asusun banki mai suna 'Daramola Cars,' kamar yadda 'Glenn Brown' ya umurta."
- A cewar sanarwar.
FBI ta samu hujjoji kan zambar 'yan Najeriya
Daramola ya tura dala 18,000 zuwa wani mai shigo da kaya daga Denmark sannan ya rubuta takardar banki ta dala 14,000.
Duk da cewa Daramola ya musanta laifin, amma FBI ta samu sakonnin WhatsApp daga wayarsa da suka tabbatar da rawar da ya taka a zambarsu.
Ogunlaja kuma ya yi amfani da asusun 'bankin Amurka' don karɓar kuɗin zamba daga wadda aka yaudara, sannan ya aika kuɗin zuwa asusun Daramola.
Amurka ta cafke dan Najeriya kan zambar $10m
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta cafke wani ɗan Najeriya, Yomi Olayeye, kan zargin karkatar da $10m na tallafin COVID-19 da aka bai wa marasa aikin yi.
Ana tuhumar Olayeye da laifuffukan haɗa baki, satar kuɗi ta intanet da satar bayanai, kamar yadda ofishin shari’ar Massachusetts ya bayyana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng