Rarara Ya Yi wa Shugaban Nijar Wankin Babban Bargo kan Zarginsa, Ya Tona Asiri
- Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi fatali da zarge-zargen da shugabanni Nijar, Abdourahamane Tchiani ke yi kan Najeriya
- Rarara ya ce wadannan zarge-zarge soki-burutsu ne kawai inda ya ce babu wanda ke cin dunduniyar Nijar kamar Tchiani
- Wannan na zuwa ne bayan Tchiani ya zargi Najeriya da hada baki da Faransa domin kawo tsaiko a mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Niamey, Nijar - Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana game da zargin shugaban Nijar kan kasar Najeriya.
Rarara ya caccaki Janar Abdourahamane Tchiai kan zargin da ya yi inda ya ce shugaban shi ne babban mai cin dunduniyar kasarsa.
Rarara ya zargi Tchiani da nakasa Nijar
Mawakn ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Babu wani mai cin dunduiyar Nijar irin Tchiani saboda irin cin amana da ya yi, mutumin da ya kwace kasa sai dai ya buya ya rika ba da umarni a boye."
"Babbar matsalarmu iyaka ne, duk dan ta'adda da aka koro sai ya fada Nijar ko Chadi, idan kuma ya fada can ba ka da izinin yakarsa sai da izinin kasar."
""Duk wadanda ke iyaka da mu renon Faransa ne, alakarmu da kasar ba ni gishiri ne in ba ka manda saboda zaman lafiyarmu shi ne alaka da Faransa."
- Dauda Kahutu Rarara
Rarara ya koka kan cin amanar Bazoum
Mawakin ya kuma yi magana kan cin zarafin da aka yiwa Mohamed Bazoum inda ya ce Tchiani ya ci amanarsa.
Rarara ya koka kan yadda al'umma ke tsoron fadin gaskiya kan mulkin Tchiani wanda hakan wasu ke ganin kaman ana goyon bayansa.
Sarakuna sun musanta zargin shugaban Nijar a Najeriya
Mn ba ku labarin cewa, wasu sarakunan gargajiya da mazauna kan iyaka a Sokoto da Kebbi sun musanta zargin shugaba Abdourahamane Tchiani.
Mazauna Balle, Marake, da Kurdula sun tabbatar da babu sansanin sojojin kasashen waje a yankunansu, sun bukaci Tchiani ya guji zarge-zargen karya.
Dagacin gundumar Balle, Alhaji Aminu Aliyu ya karyata zarge-zargen Tchiani inda ya ce babu gaskiya a maganarsa.
Asali: Legit.ng