Bidiyon Lokacin da Jirgin Kasa Ya Murkushe Wata Mota a Legas, Mutane Sun Magantu

Bidiyon Lokacin da Jirgin Kasa Ya Murkushe Wata Mota a Legas, Mutane Sun Magantu

  • Bidiyo ya nuna lokacin da jirgin kasa ya murkushe mota dauke da buhunan shinkafa a yankin Iju-Fagba da ke jihar Legas
  • Ana zargin rashin kyawun titin ne ya jawo tayoyin motar suka makale lokacin da jirgin ke isowa amma wasu na fadin akasin haka
  • Jama’a sun bayyana damuwarsu kan yawaitar hadari a Iju-Fagba, inda suka roki gwamnati ta dauki matakin gyara titin jirgin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a ranar Talata ya nuna lokacin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Iju-Fagba, jihar Legas

Motar, wadda aka ce kirar Toyota Sienna ce, na dauke da buhunan shinkafa a cikinta lokacin da hadarin ya faru.

Mutane sun yi magana yayin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Legas
Jirgin kasa ya yi karo da motar shinkafa a Legas, mutane sun roki daukin gwamnati. Hoto: @info_NRC
Asali: Facebook

Jirgin kasa ya murkushe mota a Legas

A lokacin da jaridar Punch ta tattara wannan rahoto, babu tabbacin ko an samu asarar rai ko wadanda suka ji rauni a hadarin.

Kara karanta wannan

El Rufai, Shetty da mutane 17 da Tinubu ya ba mukamai amma daga baya ya soke nadin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shekarar da ta gabata, mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da da-dama suka samu raunuka daban-daban a hadarin bas da jirgin kasa.

Bincike ya nuna cewa direban bas din BRT ne ya yi tukin ganganci, ya yi kokarin wucewa kafin jirgin ya zo, abin da ya jawo mummunan hadarin.

Abin da mutane suka ce kan hatsarin

Mutane da dama sun yi tsokaci kan hatsarin jirgi da motar shinkafar da ya faru a yau Talata.

@OgechukwuIgboa2

"Chai! Ana nufin mai motar bai ji ba, ko bai gani ba lokacin da jirgin ke busa sautin isowarsa wajen?"

@bolazeal

"Ƙuskuren gwamnati da NRC ne. Wannan ɓangaren titin jirgin ya zama tarko ga motoci. Tayar motoci kan makale a wurin saboda ramuka.
"Ina kuma shingen ƙarfe mai hana wucewa yake? Wannan abin bakin ciki ne ga kasar baki daya."

@lugbengene

"Mutane da dama ba su fahimci musabbabin wannan haɗarin ba, sai dai kawai su rika dorawa direbobi laifi.

Kara karanta wannan

'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki

Na wuce ta kan wannan titin da safe, akwai ramuka da suke riƙe motoci a kan layin jirgin. Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki don gujewa haɗari nan gaba."

@osagie_autos

"Wannan abin ya faru sau da dama. Amma kamar mutane ba sa koyon darasi daga abin da ya gabata. Lallai za mu ci gaba da maimaita kuskure da gamuwa da irin hadarin nan.
Yaushe za mu daina maimaita irin wannan kuskuren?"

@ThaMVP

"Shin haka ake gudanar da titin jirgin kasa a ƙasashen masu hankali? Ina shingen hana wucewa? Ina alamar da ke gargadin kusantowa jirgin?"

Kalli bidiyon da wani Chuks EricE ya wallafa a shafinsa na X a nan kasa:

Jirgin kasa ya murkushe mota a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani mummunan hatsari ya faru a jihar Kaduna yayin da jirgin kasa ya murkushe wata mota da ta hau kan hanyarsa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a jihar Sokoto

An ce wata mata ce ke tuka motar, kuma ta hau kan titin jirgin ba tare da ta wuce ba har ya murkushe ta a yankin Kubwa, lamarin da ya kai ga ajalin matar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.