Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Ce kan Zarginta da Shirin Ruguza Nijar da Sojojin Faransa

Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Ce kan Zarginta da Shirin Ruguza Nijar da Sojojin Faransa

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta musanta zarge-zarge cewa tana shirin tayar da rigima a makwabciyarta Jamhuriyar Nijar
  • Gwamnatin ta ce tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da samar da alaƙa mai kyau tsakanin kasashen biyu
  • Har ila yau, ta musanta cewa akwai sojojin Faransa a Arewacin Najeriya domin kawo tsaiko a mulkin Nijar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan jita-jitar neman kawo rigima a makwabciyarta Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na tayar da rikici a Jamhuriyar Nijar bayan sojoji sun karbe iko a kasar.

Gwamnatin Tinubu ta musanta shirin ruguza Jamhuriyar Nijar
Gwamnatin Bola Tinubu ta ƙaryata rade-radin tana neman ruguza Nijar da zuwan sojojin Faransa Arewacin Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Zarge-zarge: Martanin Najeriya ga kasar Nijar

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar ta bakin kakakin wucin gadi, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fita daban a Najeriya, ya ba ma'aikatan gwamnati hutun kwanaki 7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa akwai sojojin Faransa a Arewacin Najeriya da ke shirin tayar da rikici a Jamhuriyar Nijar.

Ta bayyana cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe balle makama, don haka a yi watsi da su baki daya.

“Gwamnatin Najeriya tana musanta zarge-zargen da Nijar ke yi na cewa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa, tare da taimakon wasu jami’an tsaron kasashen waje, ciki har da na Najeriya, ne suka kai hari kan bututun man fetur da ke tsakanin Nijar da Benin.
“Gwamnatin ta mika ta’aziyyarta ga gwamnatin Nijar kan wannan harin mummuna da aka kai kan bututun mai."

- Cewar sanarwar

Shirin Najeriya kan yaki da ta'addanci

Gwamnatin Najeriya ta jajirce kan yakar ta’addanci kuma ba za ta taba amincewa da ayyukan kungiyoyin ta’addanci ba, Vanguard ta ruwaito.

“Gwamnatin Najeriya tana nuna damuwarta matuka, tare da bayyana a fili cewa babu dakarun sojin Faransa da ke Arewacin Najeriya da ke shirin tayar da rikici a Jamhuriyar Nijar."

Kara karanta wannan

Alaka ta kara tsami, Nijar ta zargi Tinubu da neman kassara ta, ta gano makarkashiyarsa

“Yana da muhimmanci a jaddada cewa dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa kullum tana bisa ginshikin mutunta juna, kima da rashin tsoma baki cikin harkokin juna."

- Cewar sanarwar

Nijar ta zargi Najeriya da shirin ruguza ta

Kun ji cewa kasar Nijar ta nuna damuwa kan yadda Najeriya ke cigaba da neman kawo tarnaki ga gwamnatin sojoji a kasar.

Ministan harkokin wajen kasar, Bakary Yaou Sangare ya zargi Najeriya da hada baki da wasu ƙasashe domin kawo musu cikas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.