Fafaroma Ya Fadi Yadda Ya Tsallake Harin Kunar Bakin Wake sau 2 a Kasar Iraqi
- Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis ya bayyana yadda ya rika tsallake harin 'yan kunar bakin wake a Iraqi
- Fafaroman ya bayyana cewa sai da aka ja kunnensa da cewa kar ya ziyarci kasar, duba da kalubalen da ke tattare da hakan
- Amma an samu 'yan kunar bakin waken sun gamu da fushin 'yan sandan kasar inda aka dakile yunkurin da su ka yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Rome, Italy - Shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya tsira daga yunƙurin kashe shi har sau biyu yayin tafiyarsa mai cike da tarihi zuwa Iraqi a watan Maris na 2021.
Wannan na daga cikin abubuwan da ke cikin kundin tarihin rayuwarsa da zai fito nan gaba, wanda aka fara samun wasu bayanan da ke kunshe a ciki
CNN ta ruwaito cewa, a cikin littafinsa, Fafaroma Francis ya bayyana cewa, tawagar tsaron Vatican ta samu gargadi daga hukumomin sirri na Birtaniya cewa za a kai hare-haren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka so kashe Fafaroma Francis
American Magazine ta ruwaito cewa wata mata dauke da bama-bamai, ta nufi Mosul domin ta tashe su a lokacin ziyarar Fafaroma.
Pope a cikin tarihin rayuwarsa ya kara da cewa;
“Har ma wani motar haya ta tashi da sauri da nufin yin wannan aika-aikan.”
Jami’an Iraqi sun kashe maharan Fafaroma
Fafaroma Francis, wanda ya cika shekaru 88 a ranar Talata, ya rubuta cewa kusan kowa ya hana shi zuwa kasar Iraqi amma ya ga dacewar dole ya tafi.
Jami’an ‘yan sandan Iraqi sun yi nasarar dakile wa tare da kashe maharani kafin su kai ga idda ga mummunan nufinsu na kaddamar da harin.
Ziyarar tarihi ta kwanaki uku a cikin Maris na 2021 ta gudana ne a cikin cikakken tsaro, kuma ita ce tafiyar farko da Fafaroma ya yi cikin watanni 15.
Musulmai sun gagara mulki a Ghana
Tun daga lokacin da Ghana ta samu ‘yancin kai, ku na da labari musulmi bai taba zama shugaban kasar ba har yau duk da suna da yawa a kasar.
Wannan karo Mahamudu Bawumia ya samu kyakkyawar damar yin nasara a zaben sabon shugaban kasa amma Nana Akufo-Addo ya doke shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng